NA CE WA MIJI NA, NA GAJI DA AUREN, SAI YACE NA TAFI, YA MATSAYIN AUREN?
NA CE WA MIJI NA, NA GAJI DA AUREN, SAI YACE NA TAFI, YA MATSAYIN AUREN?
https://chat.whatsapp.com/JLojawdOWYsEOeSHZMNdjf
*TAMBAYA*❓
Assalamu Alaikum malam nice muka samu sainsa da mijina nace Masa nagaji da auren yace to shikenan natafi sai nace meyake nufi natafi ya wai tunda nagaji natafi mana amma baice ya sakeni ba to me hakan kenufi
*AMSA*👇
Wa alaikumus salamu wa rahmatullahi wa barakatuh. Alhamdu lillahi rabbil alamin wassalatu wassalamu ala rasulillahi wa ala alihi wa sahbihi ajma'in.
Amsar wannan tambaya ta dogara da niyyar mijin ki ne. Ke kika ce, kin gaji da auren, menene nufin ki? A nan duk abinda zuciyar shi ta fahimta kuma yayi hukunci da shi, shine amsar tambayar ki.
Mu sani kalmomin saki suna da yawa, amma, kalmar "saki" ita ce jagoran su kuma wacce mafi karfi da shahara a cikin su. Manzon Allah ya saki wata mata da kalmar, tafi gida ko samu iyalin ki
عَنْ عَائِشَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهَا أَنَّ ابْنَةَ الْجَوْنِ لَمَّا أُدْخِلَتْ عَلَى رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ وَدَنَا مِنْهَا قَالَتْ أَعُوذُ بِاللَّهِ مِنْكَ. فَقَالَ لَهَا: ((لَقَدْ عُذْتِ بِعَظِيمٍ، الْحَقِي بِأَهْلِكِ)).
Don haka kalmar tafi gida, saki ce, sai idan an saka sharadi, tana kuma daukar ma'anar saki, sai dai ana duba urfin mutanen gari kafin ayi hukunci da ita. Idan hakan baya cikin urfin su, sai a tambaye shi niyyar sa lokacin da ya ambata hakan.
Don haka dai, yanzu, ki koma wurin mijin ki, shine Mallamin da tabbatar maki da hukuncin auren ku duk duniyar nan, shine muftin ki, a can ne, zaki samu amsar ki mafi zama daidai da kuma dacewa.
Wallahu ta'ala a'lam.
*_Amsawa_* :
*Malam Aliyu Abubakar Masanawa*
Zaku iya samu wannan group na Facebook ta wannan hanyar👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Join us on Facebook🖕