﷽
اَلسَلامُ عَلَيْكُم وَرَحْمَةُ اَللهِ وَبَرَكاتُهُ
Daga Zauren
*📌Albahral Ilmu🌴*
*_HUKUNCIN SALLAH DA KAYAN DA AKA SAMU TA HANYAR ZINA_*
*TAMBAYA*❓
Slm Malam
Dan Allah inada tambaya
Mace ce ta kasance tana aikata zina kuma saita tuba tadena
Amma kuma acikin kayan ta na sawa dana amfani akwai wayanda ta siye su da kudin da ta samu lokacin da tana aikata zina Kuma malam idan tarabu dawayannan
Kayan tana tinanin shiga cikin wata rayuwa tarashin sittira kuma dana gudun kada wannan halin ya kuma maida ita cikin laifin da ta bari na zina
Shine take tambaya ya matsayin Ibadar ta idan tayi ta da wayannan kayan take
Kuma kudin da ta samu akwai saura a hannun ta tana so tayi siyayyar azumi dasu da kuma na sallah
Dan Allah malam tana bukatar bayani sosai akan hakan
Ka huta lafiya
*AMSA*👇
Wa'alaikumus salam Warahmatallahi Wabarkatahu. Alhamdu lillahi rabbil alamin wassalatu wassalamu ala rasulillah wa ala alihi wa sahbihi ajma'in.
Subhanallah. Idan har da gaske ta tuba ingamtacciya, ya kamata ko ganin kayan ba zata so ba, domin kawai ya dinga ɓata mata rai ke nan da haifar mata da baƙin ciki. Kuma ya kamata ta rabu da duk wani abin da zai kai ta ga tunawa da wancan lokaci ko da ta'adin da ta aikata a baya.
A gaskiya idan har tana tunanin rabuwa da wannan kayan zai sa ta koma ga aikata zinar da tace ta tuba, toh ƙarya take, ko da tace ta tuba, da baki ne kawai, bai kai zuci ba, kuma ba tayi nadama ba. Sannan a can baya, rashin tufafin ne ya sa ta zamo mazinaciya? Ƙarya ne.
Ya kamata ki sani cewa duk abin da kika samu na kuɗi da wanin su, a matsayin ladar ki ta zina, haramun ne, ci da sha, sannan babu lada idan kika yi kyauta ko sadaka da kudin zina, saboda Allah baya karɓa sai daga mai tsarki, kudin zina kuma basu da tsarki
6152 - 2044 - «من تصدق بعدل تمرة من كسب طيب ولا يقبل الله إلا الطيب فإن الله يتقبلها بيمينه ثم يربيها لصاحبها كما يربي أحدكم فلوه حتى تكون مثل الجبل» .
(صحيح) [حم ق] عن أبي هريرة. الإرواء 886، تخريج مشكلة الفقر 116.
Annabi sallallahu alaihi wa sallama yace, baya halatta, kudin kare, biyan bokanci da kuɗin karuwanci
7640 - 2760 - «لا يحل ثمن الكلب ولا حلوان الكاهن ولا مهر البغي» .
(صحيح) [د ن] عن أبي هريرة. أحاديث البيوع.
Ƙa'ida ita ce, duk wanda ya nemi dukiya ta hanyar haram, alhali yana sane da cewa haramun ne, toh idan ya tuba, wajibi ne ya rabu da dukiyar nan. Amma idan baya da masaniyar cewa hanyar da ya nemi wannan dukiya haramtaciya ce, toh idan ya tuba, zai riƙe dukiyar ne, ya amfana da ita.
Don haka wannan kuɗin na zina ya zamo wajibi ta rabu da su, domin kuwa ta san cewa zina haramun ce, haka tara dukiya ta hanyar zina haram ne. Mallamai sun yi amfani da ayar alqur'ani da tace, mai riba idan ya tuba, toh ya riƙe uwar kudin sa, amma ya rabu da abin da ya hau na haramun (ribar).
(... وَإِن تُبۡتُمۡ فَلَكُمۡ رُءُوسُ أَمۡوَ ٰلِكُمۡ لَا تَظۡلِمُونَ وَلَا تُظۡلَمُونَ)
[Surah Al-Baqarah 279]
Amma Shaikhul Islam Ibnu Taimiyyah yana da fahimtar idan tubabben matalauci ne kuma zai tagayyara idan ya rabu da dukiyar haram din, toh yana iya riƙe ta ya amfana da ita.
Daga ƙarshe zata iya siyayyar azumi da na sallah da sauran kuɗin, ta raba ma bayin Allah.
Ya Allah ka nisanta mu da zurriyyar mu daga aikata zina, Allah ya gafarta maki da mu duka.
Wallahu ta'aala a'lam.
*_Amsawa_* :
*Malam Aliyu Abubakar Masanawa*
Ga ma su sha'awar shiga wannan group sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu ta WhatsApp