*HUKUNCIN WANDA KE YAWAN KOKWANTO ACIKIN SALLARSA :*
https://chat.whatsapp.com/LRPQDrs7qSoKXuSspoPkFm
*TAMBAYA*❓
As Salam alaikum Malam, ina da tambaya game da yawan kokonto cikin sallah musamman idan ban sami yin Sallah a cikin jam'i ba. Sai shaiɗan ya ke wasa da hankali na kan ko na yi mantuwa ban cika sallar ba ko kuma na ƙara. Yaya zan yi akan wannan lamarin?
*AMSA*👇
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.
Wanda ya samu irin wannan matsalar, Malamai suka ce ya rika kokarin cire wannan kokwanton daga zuciyarsa.
Idan kuma har ya gagara yin hakan, to sujadah ba'adiy zai rika yi duk sanda ya idar da sallah. Koda kuwa kokwanton cikin tauye sallar ne, ko Qara wani rukuni a sallar.
Mutane da yawa suna fama da irin wannan larurar amma za'a iya magance abun ta hanyoyi kamar haka:
1. Yawaita zikirin Allah akoda yaushe tare da yawaita karatun Alqur'ani a kullum.
2. Yawaita yin nafilfili acikin gida musamman a tsakar dare da kuma yin nafila amasallaci kafin sallolin farilla. (wannan zai fusata shaidanin dake sanya kokwanton har ya razana ya gujeka).
3. Ka rika kokarin karyata kokonton aduk sanda ya darsu a zuciyarka. Tare da neman taimakon Allah da tsarewarsa daga sharrin shaidan (kayi isti'aza sau uku kamar yadda Annabi ﷺ ya koyar) koda kuwa atsaye kake a sallar ko a zaune ko cikin sujadah.
WALLAHU A'ALAM.
Zaku iya samu wannan group na Facebook ta wannan hanyar👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Join us on Facebook🖕