WANE IRIN ALBISHIR MANZON ALLAH (SAW) YAKE YIWA AL'UMMARSA KAFIN ZUWAN WATAN RAMADANA?
https://chat.whatsapp.com/IQUc0RxgCwA3JFiEKl8j5E
*TAMBAYA*❓
Assalamu alaikum warahmatullah. Wane irin albishir Manzon Allah yake yiwa al`ummarsa kafin watan Ramadan ya kama?
*AMSA:*👇
Wa alaikumus salam, Manzon Allah (SAW) ya Kasance yana yiwa al`ummarsa bushara da zuwan Ramadan. Kamar yadda hadisi ya tabbbata daga Abu Huraira yace: naji Manzon Allah yana cewa:
*إِذَا دَخَلَ رَمَضَان ُفُتِّحَتْ أَبْوَابُ الْجَنَّة ِوَغُلِّقَت ْأَبْوَابُ جَهَنَّم َوَسُلْسِلَت ْالشَّيَاطِينُ*
Ma’ana: _Idan watan Ramadan ya shigo ana buɗe qofofin rahama da qofofin aljanna,
kuma ana rufe qofofin jahannama, kuma
ana ɗaure shaiɗanu._ Bukhari suka ruwaito shi a lambata 3277 da Muslim a lamba ta 1079.
Haka kuma an ruwaito daga Anas Ibn Mālik yace (Watan) Ramadan ya shigo sai Manzon Allah yace: Haqiqa wannan wata (na Ramadan) ya halarto muku, acikinsa akwai wani dare wanda yafi watanni dubu alheri. Duk
wanda aka haramta masa (samun
alherin da ke cikinsa) haqiqa an haramta
masa alkhairi dukansa. Kuma babu wanda ake haramtawa alherinsa sai
wanda bashi da rabo. Ibn Majah ya ruwaito shi kuma Albani yace hadisin hasan ne.
Allah ne mafi sani.
Zaku iya samu wannan group na Facebook ta wannan hanyar👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Join us on Facebook🖕