JAMB REGULAZATION



✔️JAMB REGULAZATION✔️

✔️Menene jamb regulazation❓
✔️Yaya ake yin jamb regulazation❓
✔️Meye amfanin jamb regulazation❓
✔️Jamb regulazation ya kasu Kashi nawa❓
A Ina ake yin Jamb regulazation❓
✔️ Su waye ke yin jamb regulazation❓

1. Menene jamb regulazation❓

Jamb regulazation abu ne da dalibai wadanda sukai karatu a makarantu na gaba da sakandare (Tertiary institution) Wanda ba Jami'a ba,Kuma Suna son su cigaba da karatunsu matakin Jami'a bayan sun kammala karatun NCE ko ND.

2. Yaya ake yin jamb regulazation❓

Da farko ka tabbatar ka kammala karatunka na NCE ko ND, sannan sai ka garzaya jamb office ka ce zakai jamb regulazation, daga Nan zasu turaka banki ka aiye Jamb Pin, idan ka dawo zasu maka/ki abunda kake bukata. Kafin ka tafi ka tabbatar ka tafi da
 A. Dukkanin takardunka na ainihi(Original copy)
B. Hotuna kanana(Passport) 
C. Lambar waya
D. Gmail account
E. A level certificate (Original)
F.Jamb pin
G. Lambar makaranta(Previous Admission Number)
H. Combination/Course
I. Sunan shugaban makaranta
J. Lamabarsa
K. Makin da ka kammala dashi(Grade)
L. Adireshi. 

Ka tabbatar duk bayanan da zaka bayar Yana daidai da sauran bayananka na baya.

Bayan duk kayi hakan wadansu jamb office na jahohi zasu baka wata Takarda Mai dauke da bayananka sai turaka makarantar daka kammala ka Kai masu ita a ofishin Shugaban makaranta ko Kuma shugaban gudanarwa.(Academic secretary).,wasu Kuma Jamb office na jahohi su zasu Kai maka takardan da kansu a makarantarku. 

Bayan duk kayi hakan sai ka rika duba Gmail address naka don ganin ko an turomaka jamb Number naka sai ka je ka fiddota ka jira Jami'ar da kake bukata. 
Wannan numbar da zaa turomaka a Gmail address ita ake Kira Jamb Number wadda tana da lamba guda takwas da Kuma wasu haruffa guda biyu a gaba.

3. Meye amfanin jamb regulazation❓

A dokar kasa ta ilimi Babu Jami'ar da zata baka admission ba tare da jamb Number ba.

Dama Ana yin jamb Number ne akan dalilin baka da ita tun farko ko Kuma kana da ita a baya Amma jamb office Basu da bayananka.

Haka Kuma Sai da jamb Number zaka je Aikin yiwa kasa hidima(NYSC)

Amma ku lura cewa akwai wadanda zasui jamb regulazation kafin su shiga Jami'a bayan sun shiga sai Kuma su ji ance hukumar jamb batasan dasu ba,toh Wannan ma Mai sauki ne ka garzaya ka tafi jamb office ka masu bayanin hakan sai dai Kar ka kuskura ka kammala karatunka bakayi ba saboda bazaka je NYSC ba sai da ita.

4. Jamb regulazation ya kasu Kashi nawa❓

Jamb regulazation ya kasu Kashi biyu

A. Wanda ake kafin ka shiga Jami'a
B. Wanda ake yi Bayan ka samu gurbin karatu a jami'a,saboda matsalar ba jamb ta baka gurbin karatu ba. Idan hakan ya faru dakai kayi kokari kaje jamb office don bada rahoton matsalarka. 

5. A Ina ake yin Jamb regulazation❓

Dokar kasa ce ta hukumar jamb duk Wanda zai Yi Jamb regulazation ya tabbata ya tafi Jamb office don yin duk abunda yakamata.

6. Su waye keyin jamb regulazation❓

Kamar yanda muka fada a baya cewa wadanda ke yin jamb regulazation su ne daliban da suke son shiga Jami'a Basu da jamb Number Kamar masu NCE ko ND. Ko Kuma makaranta ce ta Basu admission ba hukumar jamb ta.

Naku har kulum 
Comr Rufai Abdullah Dole
08162852416
26 March. 2021
Post a Comment (0)