*MAGANIN RAGE QIBA IN SHA ALLAHU*
:
Daga Zauren
Khulafa'ur-rashiidun.
.
HANYOYIN RAGE QIBA
:
Assalamu Alaikum warahamatullahi wa barkatuhu, hadin duka maza da mata suna iya mafani dasu, sannan kayan hadin sekuje islamic Medicine, ko yan kayan yaji (na miyya), sannan zan zayyano, kala kala, seku rubuta a takadda dan whatsApp beda tabbas!!!
:
1) *Lemun zaqi 1*
*Lemun tsami 1*
*Zuma cokali 3*
*Citta danya guda 1*
*Ruwa 50cl, kaman* gorar pepsi.
Ki wanke lemunan duka seki yanka ki rabasu hudu, amma ba sekin cire bawon ba seki zuba ruwan, ki gurza citta ki zuba ki kawo zuma kisa, seki dora awuta kisa wutar kadan, harse ya dahu seki sauke, ki bari ya sha iska seki muttsuke ki tace kisha. *Yana rage qiba sosai* in sha ALLAHU, inkuma kinaso kiyi da yawa ne toh seki sa kome kaman yanda na fada sannan ki dura a goruna kisaka a fridge kullum kisha safe dare so 2 a rana kenan. (Maza ma suna iya amfani dashi).
.
2) *Apple cider vinegar*
A gora yake, zaki zuba marfi 3 na goran acikin kofi 1 na ruwan zafi seki sha so 2 a rana, idan kuma hada tumbi toh seki riqa shafawa a tumbin. Wurin masu saida su salad cream dasu mayon naise, *nan zaki samu apple cider vinegar.*
3) *Grape fruit* (lemun taba)
Cinnamon (karfi)
Zaki bare bawon lemun taba sannan ki yanka lemun kihada da cinnamon ki dora a wuta, cinnamon inkin daka shi toh cokali daya zakisa, *lemun kuma guda daya ruwa kofi 1,* idan ya dahu seki sa zuma kisha.
.
4) *Zogale danyen ko busasshe seki daka in busasshe ne*, inkuma danyene seki markada ki matsa lemun tsami guda 1 seki riqa sha da safe kafin kici kome, sekuma dare inzaki kwanta.
.
5) *Habbatus sauda capsules*
*Zaki riqa shan su so uku a rana, biyu biyu zaki riqa sha, kuma ba rage qiba kadai yake ba zaki ji baki jin nauyin jikinki,* habba nada magunguna da yawa a jikin dan adam.
.
6) *Lipton wanda aka rubuta (yellow label) ki dauka guda 1 kisa ruwa kofi 1*, kanunfari dan dai dai, se lemun tsami rabi, in kuma baki da ulcer kisa 1, se zuma cokali 2 seki dafa a tare in ya dahu seki sha. *Shima so biyu a rana*.
.
7) Amfani da koren shayi (green tea) yana rage qiba sosai, *IN SHA ALLAHU*, a shashi da ruwan zafi ba tare da ansa kome ba.
.
8) Ginger tea (shayin citta)
*Citta danya guda 1*
*Lemun tsami 1*
*Ruwa kofi 4*
*Zuma cokali 1*
Ki dora ruwa se yayi kaman ze tafasa seki yanka citta ki zuba yakai kamar minti 10 akan wuta seki sauke, ki yanka lemun tsami yankan yayi fale fale seki saka acikin ruwan da kika sauke, sannan kisa zuma ki motsa kisha da duminshi.
.
9) Wata hanyar hadin danyar citta kuma:- *ki nuqa citta da abun nuqa agushi na cikin blender,* ko kuma turmi amma wurin nuqan kada asa ruwa, in ta nuqu seki saka tafasasshen ruwa kamar kofi 1, seki rufe yakai kaman minti 30, seki samu lemun tsami guda 2 ki yanka yankan round seki samu jug ko wani abu me marfi ki zuba yankakken lemun tsamin seki dakko wannan cittan seki tace acikin lemun tsamin seki qara ruwa kaman kofi 2! seki rufe ya kwana. In gari ya waye seki bude ki zuba garin cinnamon cokali 1, ki motsa sosai ya qara kwana seki sha.
.
10) Man zaitun, lemun tsami.
*Ki zuba man zaitun cokali 1, ki matsa lemun tsami rabi kiriqa shan haka so 3 a rana.*
.
Green tea :- yana nan ana saida shi a kwali, ya zamana kina sha da ruwan zafi so 2 a rana, ya kasance shine tea dinki, maimakon tea da zaki sha me madara. *Kuma inkinso zaki sa sugar ko kuma zuma, in da safe ne zakisha toh seki hadashi da* (cabin biscuit) ko kuma crackers, maimakon kici da bread don bread yanasa qiba.
.
11) *Danyar citta 2*
*Lemun tsami 1*
*Zuma cokali 4*
Ki kankare citta seki yanyanka ki saka a mixer cup, seki 6are 6awon lemun tsamin seki yanka ki hade shi cikin yqnkakkiyar cittan seki zuba zuma itama duk wuri daya seki mixing da mixer. *In kuma turmi ne toh ba zaki zuba zuma ba har sekin gama kuma ana so suyi laushi sosai don ba'a tacewa,* inkika gama seki samu kolban mayonnaise wadda ba kome aciki seki juye wannan hadin naki, ki saka a fridge, ba fa freezer ba seki sa ya kwana 1, *kullum seki dibi karamin cokali na shan tea kisha so uku a rana.* Amma inzaki sha da dare toh kisamu kamar minti 30 kafin ki kwanta!!!. (Haka namiji mazeyi)
12) *Lemun tsami 1*
*Danyar citta cikin cokali 1*, in an gurzata. Cocumber 1
*Aloe vera ruwan ta cikin cokali 1*
Na'a na'a garin shi cokali 1.
Duk in kin tashi kiyi blending dinsu gaba daya seki saka a fridge, in kin tashi cin abinci seki ajeshi kusa da ke, kisha kafin cin abinci
.
13) Sassaqen gamji a tafasa shi da jar kanwa 'yar kadan se a riqa sha, yana kone kitse sosai.
Wadannan abubuwan dana zayyano duk hade suke da rage tumbi, mace da namiji duk zasu iya amfani dashi.
.
Sannan masu qiba se sun kula sosai da irin abinda sukeci ko suke sha, wanda ke neman rage qiba dole ya rage cin wadannan abubuwan
A) A taqaita shan madara, milo, ovaltine, bournvita, akoma ma shan green tea kadai kamar yanda nai bayanin shi a sama.
.
B) Kiyaye naman kaza musamman masu ci akai akai, a riqa cin su kifi 'yan shila, naman rago in an cire kitse. !!!
.
C) Madarar shanu, kindirmo, su abinda ya shafi alkama, bread, duk se an kiyaye wadannan indai anaso a rage qiba
.
D) In kina cin abinci cikin plate 1,toh ki rage ki koma rabin plate seki sa latas da su Cocumber. *Haka in shinkafa ce koda fara kika dafa toh ki steaming din alayyahu, ko zogale, kici dashi*, wato ki turara.
.
E) Kada ki bari wadannan abubuwan su riqa qare miki musamman in kinaso ki rage qiba, *wato su zogale, latas in lokacin shine, cocumber, alayyahu, rama /matse, uwa uba kuma fruits son samu kullum kisha.*
*Sannan ki daure kiriqa ayyukan gidan ki da kanki ze temaka miki sosai, kai kawo yana hana qiba ta samu wurin zama, ALLAH ya yaye ma masu fama da ita, don qiba cuta ce.*
SANAR WA MACE ME CIKI TA HAKURA DA SHAN WANNAN HADIN
--------------------------------
* �MAMAN AMIIR*
https://youtu.be/mC2nNHuGHAo
________ ___________
ﺳﺒﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ، ﺍﺷﻬﺪ ﺍﻥ ﻻ ﺍﻟﻪ ﺍﻻ ﺍﻧﺖ ﺍﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺍﺗﻮﺏ ﺍﻟﻴﻚ ،
Kuna iya samun mu ta facebook
https://mobile.facebook.com/khulafaurrashidun/ ?