MARHABAN RAMADAN

⚖️
*HAMDALA WRITIN'S ASSOCIATION💪*
        _*{{RUBUTU DOMIN CIGABAN AL'UMMA📚}}*_
https://www.facebook.com/111403834371046

             *✨✨{{H.W.A}}✨✨*
     https://chat.whatsapp.com/IfZVNIt6C9S8PvTV10v3wZ

 *🌷MARHABA RAMADAN🌷*

Shiri akan kiyaye                           
        *SALLAH*

*Writing by Oum kadijat*
 
*Kashi na 1*
Muhimmanci sallah acikin addinin musulunci

 *Sallah* rukuni daya daga cikin rukunan musulunci guda biyar wadda itace tazo a rukuni na biyu itace cikar imanin duk wani musulmi itace ibadar da take kusantar da bawa ga mahaliccinsa  

Sallah ce tahƙiƙanin bambanci tsakanin Musulmi da wanda ba Musulmi ba. Ita ce jigon imani, Saboda darajar sallah Allah (s w t)Acikin Littafinsa Mai tsarki A suratul Baƙara, aya ta 238. Allah ya umarce mu cewa:


*حافظوا على الصلوات والصلاة الوسطى وقوموا لله قانتين*

*Ku tsare lokatai a kan salloli da Sallah mafificiya. Kuma ku tsayu kuna ma su ƙanƙan da kai ga Allah.*


  Cewar Annabi Muhammad tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi.  

"Acikin ayyukan da bawa ya aikata abin da za a fara dubawa A ranan Al-ƙiyama shi ne sallah. Idan aka dubawa bawa sallarsa akaga ta yi kyau, to lallai ragoyin ayyukansa zasu kasance masu kyau;Idan sallar bawa ta baci to lallai ragoyin ayyukansa zasu kasance batattu, Sadaqa Rasulil kareeem.

    An ruwaito daga ibnu Mas'ud, yardar Allah ta tabbata a gare shi, watarana"wani mutum ya tambayi ma'aikin Allah, tsira da Amincin Allah su kara tabbata a gare shi, cewa, "ya Manzon Allah, wane aiki ne ya fi sauran ayyuka?" Sai ya ce, "yin Sallah a cikin lokacin ta".
     Sallah kam ibada ce ta ruhu wadda idan aka tsayar da ita da sharuɗan ta, kuma da zuciya guda gami da natsuwa. Za ta zama mafarin samun shiriya da nisantar miyagun ayyuka, kamar dai yadda Allah ya ce a cikin suratul Ankabut, aya ta 45:


*واقم الصلاة إن الصلاة تنهى عن الفحشاء والمنكر، ولذكرالله اكبر، والله يعلم ما تصنعون*

*Kuma ka tsayar da Sallah. Lallai sallah tana hanawa daga alfasha da abin ƙi, kuma lallai ambaton Allah ya fi girma, kuma Allah yana sane da Abin da kuke aikatawa.*
Sadaqallahul Azeem

            Sallah ibada ce ta zuci da ta jiki. Mai yin ta zai haskaka da hasken Allah. Yin Sallah shi ne babbar alamar cikar imani, mafi darajar hanyoyin Ibada, 

Kuma hanya mafi tabbatar da nuna godiyar bawa ga Allah saboda tarin baiwar da ya yi mana. Yin watsi da Sallah yana nesanta mutum da Allah, ya rasa rahamar sa da falalar sa da jin ƙan sa sannan zai gamu da Azabar Allah😭
      
      Martabar Sallah ta kai ma cewa mutum ba ya iya barin ta acikin ko wane hali ya sami kansa. Dole ya kawo ta ko yana tafiya ko yana gida, ko cikin tsoro ko cikin aminci. Allah ya faɗi a suratul Baƙara, aya ta (238) da (239)


*حافظوا على الصلوات والصلاة الوسطى وقوموا لله قانتين, فان خفتم فرجالا أو ركبانا، فإذا امنتم فاذ كرواالله كما علمكم مالم تكونوا تعلمون*

*Ku tsare lokatai akan salloli da Sallah mafificiya. Kuma ku tsayu kuna ma su ƙanƙan da kai ga Allah. To, idan kun ji tsoro, to (ku dai yi sallah gwargwadon hali) da tafiya ƙasa ko kuwa a kan dabbobi. Sa'an nan idan kun amince, sai ku ambaci Allah kamar yadda ya nuna muku abin da ba ku kasance kuna sani ba.*

Sadaqallahul azeem**
            Ya "yan uwa mukula da sallah muyita acikin lokacin ta kar mubari lokacin sallah ya kubce Mana idan bada kwakkwaran laluraba  
       
Allah yasa mu dace Allah ya bamu ikon kula da lokacin sallah.
Alhamdulillah,Abunda muka fada daidai Allah ya bamu lada kuskuren dake ciki Allah ya yafe mana👏👏👏


Post a Comment (0)