SHIN YA HALATTA A JINGINA ƊAN ZINA GA UBANSA?
https://chat.whatsapp.com/IQUc0RxgCwA3JFiEKl8j5E
*TAMBAYA*❓
Mutum ne yayi zina da Mace har tasamu ciki, kuma yace ya yarda yakarbi cikin idan ta haihu yanason dansa, Shin a Shari'ance yana halatta ajingina wannan dan zinar zuwaga Ubansa na zinar tunda yakarba kokuma a'a bai halattaba??
:
*AMSA*👇
:
Mālamai sun ƙārawa jūna sani dangane da hukuncin jingina Ɗan-Zina zuwaga ubansa, dafarkodai dukkan Mālamai sunyi Ittifāƙi akan cewa idan Mutum yayi zina da Mātar aure to ana jingina ɗantane zuwaga mijinta bawai wanda yayi zinar da'itaba, koda kuwa wanda yayi zinar da'ita tasamu cikin yayi da'awar cewa cikinsane, to baza'ayi aiki da maganarsaba matukar dai tahaifi yaron acikin watanni shida ko sama dahaka bayan aure, to za'a jingina wannan ɗan zuwaga mijinta, saidai idan mijinne yakore ɗan ta hanyar Li'āni a kotu,
:
Sannan idan yakasance Mātar bata da aure kuma wanda yayi mata cikin bai yarda cewa nasa bane, kokuma yaƙi yarda yakarbeshi amatsayin ɗansa, to ananma Ƙaulan-Wāhidan Malamai sukace baza'a jingina wannan Ɗan-Zinar zuwaga wanda yayi mata cikinba,
:
Amma idan wanda yayi mata cikin yayarda cewa shine yayi, kuma ya yarda yakarɓi cikin amatsayin ɗansa, to anan sai Mālamai sukayi Sāɓānī, mafi yawa daga cikin Mālamai cikinsu harda gālibin Malaman dake Mazhabobinnan guda hudu, duk suntafine akan cewa baza'a riskar da Ɗan-Zina zuwaga ubansa ba koda kuwa uban yakarɓi cikin ya yarda cewa Ɗansane, sukace baza'a jinginashi zuwa gareshiba, daga cikin Dalilansu sunkafa Hujja da wannan Hadisin da Annαвi( ﷺ ) Yace:
:
ﺍﻟﻮﻟﺪ ﻟﻠﻔﺮﺍﺵ ﻭﻟﻠﻌﺎﻫﺮ ﺍﻟﺤﺠﺮ ،
:
MA'ANA:
Ɗa namai-Shinfiɗane (mijinta ko shugabanta idan baiwace) shikuma wanda yayi zina sai ayimasa Hajaru (idan ansamu shaidu kuma yataɓa aure)
:
Malaman dasuke kan wannan fahimta awajensu baza'a jingina Ɗan-Zina zuwaga ubansaba, hakanan babu gādo tsakanin Ɗan da Uban saidai yagāji uwarsa kawai,
:
To Saidai kuma agefe ɗaya akwai Mālaman da suka tafi akan cewa ana iya jingina Ɗan-Zina zuwaga ubansa matuƙar dai uban yayi da'awar cewa nasane kuma yakarɓa, Malamai da yawa kamar irin su
Ibn-Taymiyya,
Ibnul-Ƙayyum,
Hasanul-Basariy,
da wasunsu suna ganin hakan babu laifi musamman idan ya kasance akwai wata Maslaha ta rayuwa da aka kalla, shiyasa ma sukace ya halatta adauramusu aure bayan yayi mata cikin, daga cikin Dalilan Malaman dake kan wannan ra'ayi sunkafa Hujja dacewa asali an halicci wannan yarone da ruwan maniyyin wanda yayi zinar da'ita, kuma ya yarda cewa nasane, sannan sukace ai wancan Hadisin da Annαвi( ﷺ ) Yace:
:
ﺍﻟﻮﻟﺪ ﻟﻠﻔﺮﺍﺵ ﻭﻟﻠﻌﺎﻫﺮ ﺍﻟﺤﺠﺮ ،
:
Yana magane akan idan mace tanada mijine kaɗai, amma idan bata da miji to Zāhirin Hadisin baya nuna cewa idan mutum ya yarda cewa ɗansane kada ajingina masa shiba, danhaka sukace indai har mutum yāyi iƙirārin cewa ɗansane to za'a jinginashi zuwa gareshi sannan kuma akwai gādo atsakaninsu:
:
шαʟʟαнυ-тα'αʟα α'αʟαмυ
Ga ma su sha'awar shiga wannan group sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu ta WhatsApp
08087788208
08054836621
*_Group Admin: 👇_*
*MAL. HAMISU IBN YUSUF*