A KULA DA MAGAUTA DA MAHASSADA YAYIN BINCIKEN AURE


*A KULA DA MAGAUTA DA MAHASSADA YAYIN BINCIKEN AURE*

https://chat.whatsapp.com/J1hm5Tw12uYBqfaiPwf28l

*TAMBAYA*❓

Assalamu Alaikum dafatan katashi lfy, Allah yakara basira. Don Allah ina so a amsa mini wannan tambayan ko abamu shawara, ina da abokina/amini na mun tashi tare mun yi karatu tun daga matakin primary har zuwa jami'a tare muka gama, mun zama kamar yan uwa. Abokina yayi aure wata hudu da suka wuce kuma daga baya yake samun labarin matar tashi bata kama kantaba kafin ya aureta, Harma ya hadu da wassu daga cikin wadda suka sadu da ita kafin ya aureta, kasancewa ba a gari daya suke ba a makaranta suka hadu, kuma yayi iya binciken halinta kafin ya aureta amma bai gano rashin kamun kantaba.

Kuma a halin yanxu yace ta fita a ransa tun da yaji labarin abubuwan da tayi a baya, A matsayina na amininsa nace kar yayi hukuncin da babu shi a sharia da sunnah ya bari mutura tambaya a malamanmu na sunnah domin samun cikekkan amsa da shawarwari. Nagode

*AMSA*👇

Wa'alaikum assalam, Mutukar ta tuba, kuma ingantaccen tuba ne, zai iya cigaba da zama da ita, saboda wanda ya tuba daga zunubi kamar wanda bai taba aikatawa ne ba.

Saidai in har ya daina sonta kwata-kwata, to rabuwa ita ce mafita, saboda duk matar da ba ka so, to za ba ka iya tsayawa da hakkokinta ba.

Rayuwar aure tana ginuwa ne akan soyayya da sha'awa, idan daya ya samu tangarda, aure ba zai tafi a SAITI ba.

Allah ya shar'anta saki ne saboda tunkude cuta daga ma'aurata ko kuma daya daga cikinsu.

Ina baka shawara da ka kara bincike da nazari saboda Makiya da Mahassada da Magauta suna iya bata mutum da tsagwaron Kage.

Allah ne mafi sani.

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.

‎Ga ma su sha'awar shiga wannan group sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu ta WhatsApp
08087788208
08054836621
 *_Group Admin: ▽_*
 *MAL. HAMISU IBN YUSUF*
Post a Comment (0)