A RIQA DUBA ME KA YI

A RIQA DUBA ME KA YI

In dai mace ce, ka yi abin da ya zama wajibi a kanka kawai, ka dauka cewa duk abin da kake mata ba don ita kake yi ba, da farko dai don Allah ne, na biyu kuma kana son ka gyara gidanka ne, in har za ka riqa ba iyalinka abu kana dubawa nan gaba har gori za ka riqa yi, cewa "Ashe ban yi miki kaza da kaza ba?" Hakan kuma ba dabi'ar namiji ba ce, ka yi abin da ya dace kawai, ka nuna qaunarka kare ta, za ta ji dadi ta dage wajen kyautata maka ita ma.

To bare kuma komai ka yi wa iyalinka, duk da cewa haqqinta ne a kanka sai ka yi, Allah kuma zai ba ka lada a kai, wani hadisi da Buhari da Muslim suka rawaito Annabi SAW yana cewa "Ba wani abu da za ka ba wa iyakinka wanda kake neman fuskar Allah da shi sai an ba ka ladarsa, har lomar da za ka saka a bakin matarka" ban sani ba ko shi ne na ga Larabawa suna yanko loma su sa a bakin matansu, ko ka taba gwadawa? A hadisin Muslim fa jima'i da za ka biya wa kanka buqata ma lada za a baka, Allah sarki!

Zamuci gaba insha Allah.

*Gabatarwa: Zauren Sunnah*

*WhatsApp @Zauren Sunnah*
 +2348039103800.
 +2347065569254

*follow My Facebook Page*
Visit to Like my Page-https://www.facebook.com/100625758324355?referrer=whatsapp

*Facebook @Zauren Sunnah*
https://www.facebook.com/groups/552998655501583/

*Telegram: @Zauren Sunnah*
https://t.me/joinchat/AAAAAFCIDJerVcs_IP1D9g

*وسبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا اله إلا أنت استغفرك وأتوب إليك. وأستغفر الله لى ولكم ولسائر جميع المسلمين من كل ذنب و استغفر وه إنه هو البرالرحيم*

*_والسلام عليكم ورحمة الله وبركاته_*


Post a Comment (0)