🍁🌴 *AKAN ABAYA HARDA ZINA A RAMADAN*🌴🍁
AREWA AKWAI KURA
by *miss untichlobanty*
Kaman Sati daya da ya wuce it has came to my knowledge that matan arewa are planning to wear abaya which made me to re think my decision to wear it this yeae as I always do every Eid however the positive side of me was happy thinking that they have hope they are starting to migrate daga Dan iskan Riga da skirt zuwa abaya with time za'a koma hijabi. What happened next will shock you!
As I log to Instagram yester-night and started responding to my pending Direct messages. I saw 5 message from a brother and it ended with "please save my sister" that got my attention that I had to check it.
The brother said that since a week before Ramadan started many girls were planning to buy abaya and that became a trend however it has got so serious to the extent that they could do any thing when I say anything I mean anything to get abaya. Including zina.
His elder sister wanted one so badly but they are orphans they stay with their grandmother and can't afford one. So as he was returning from market yesterday bayan sallan la'asar zai shiga zaure yaga yayar sa ta rako kawar ta da alamu tafiya zatayi tsayawa yayi bai shiga ba saboda jin me suke cewa inda yayr shi ke fadin ita fa ko bashi ne zata ci Dan ta siyo abayar nan. Her friend said she doesn't need loan ta siya da kudin ta zata siya yayar tasa tace ta ina zata samu dubu 20 kamain Ramadan ya kare ita da yanzu haka dukiyar ta 200 ne kacal. Budan bakin kawar nan nata sai fadi tayi "ke a ganin ki sauran yan matan da suka siya aiki sukayi ke bakisan abinda ake yayi ba yanzu? Ai yadda aka samu iPhone haka za'a samu abaya kawai wani Gaye zaki samu kuyi dashi ya baki abaya ki bashi abun. Yayar tasa da sauri ta girgiza kai tace ma kawar nata baza ta iya ba ita duk iskanci ta bai kai nan ba a barta de a tabe tabe amma bazata iya zina ba.
Wannan kawar nata sai cewa tayi aiko bazaki sa abaya ba. Har ta fara kokarin fita yayar tasa tace ma kawar ta ba wani hanya sai wannan tabe baki kawar tayi yayar tashi daga karshe de tace ta yarda amma ta rufe Mata asiri kar kowa ya sani.
Brother nan yace be ma San me yake ji ba ya ma kasa motsi kawai ya fashe da kuka. Kokarin zuwa yayi ya fada wa kakar su ta rikoshi ya hankade ta koda ya fada kakar tace kalleta zasuyi a gida a karo na biyu ta kara basa mamaki sai cewa tayi bata ga uban da zai hana ta saka abaya da sallah ba ...
Ji nayi kamar wasa abin Dan ba yarda ba ma saide me koda na duba sai naga ana ta yi wa yan Mata wa'azi cewa su daina bada budurcin su saboda su siya abaya. Zuciya na yayi nauyi saboda ganin mutunci da ake yiwa Allah.
Yanzu ke hamshakiya wai dole sai kinyi PARTICIPATING a abaya challenge bakida hanakali ne? Ko kuwa kina da shi amma kin bada aro?
Na farko dai anyi don't rush challenge yanzu zaki iya tuna Wanda sukayi? Shi kanshi challenge din ma kin mance da shi saboda yayin shi ya wuce. Matan aure suka fito suka zubda mutunci akan wani Dan iskan mawaki da wakarsa something gimbiya hausa yanzu wa ma yake tunowa kinga an mance toh abaya challenge dinma haka zai wuce kuma ya wuce da mutuncin ki. Shi wannan saurayin da ya siya miki kina tunanin yana ganin ki da mutunci? Ai yadda ya baki abaya ko ba Dade ko ba Jima sai kin biya. Ke ko kin samu kunyi aure sai ya gasa ki. Me yasa zaku ga wasu mazan suyi ta narka wa matan su duka? Ayi ta cewa da sonta yake kaza kaza saboda bakida kuma a wajen shi yasan abin duniya kike so. Ke kinsan menene zina kuwa? Mazinaciya fa in ta mutu bata tuba ba dole sai ta je wuta, kuma ko kin tuba kin Riga kin zuba wa kanki guba. Saboda in dai a rayuwar ki kin taba yin zina toh kin Riga kin hallaka zumunci a tsakanin zuri'ar ki. Sai kuga yan uwa kaman makiya kullum ana tashin hankali ba zaman lafiya a binciki uwar su,idan kika samu sukayi zaman lafiya toh ke bazasu dauke ki komai ba suna da kudi da komai amma su barki da cin gaya.
Idan kika samu suka daraja ki toh bazasu dauki yan uwanki da daraja ba zakiji Anna yasin haushin kanwar babata nake ji. Ke mazinaciya zama a cikin al'umma ma masifa ce garesu saboda albarka baya sauka a inda take shiyasa duk yadda musulunci yake nuni da a daraja dan Adam har kafiri mazinata da Allah ya tashi cewa yayi a gillaza musu, a wulakanta su saboda gaiyan asara ne dabba ma ta fisu daraja sannan mazinaciya a farjin ta za'a sakala mata kugiya wato hook a rataye ta a wuta .
Shin kinsan cewa mutane masu bin yayi da son abin duniyan nan manzon Allah ya tsane su? Ku duba duk kirki, tausayi da mutunci wa yakai manzon Allah? Amma yace irin mutanen nan ko basuda lafiya kar Allah yasa su warke. In takaici ne dasu kar Allah yasa su samu kudi atakaice ko wani matsala irin mutanen nan suka shiga kar Allah ya fitar dasu. Idan ba butulci irin na Dan Adam ba Allah ya baki ji wani kurma ne ya baki gani wani makaho ne , kina nan garai dake wani jikin sa ya shanye kina lafiya wani yana gadon asibiti ko abincin nan kyauta Allah ya baki saboda yaga dama duk kudin naki in abincin basu tsiro ba me zaki siya? Numfashi wannan kyauta kike sha wani sai ya biya 3500 per hour Wanda yake 84,000 per day a hospital kina raye wani tun yana yaro ya mutu wani ba'a haifeshi da rai ba amma yafi Wanda barin sa akayi Wanda barin sa akayi wani kuma shege ne bayida uba. Amma a haka yafi Wanda uwar sa tayi cikin shegen kuma taje asubiti akasa karfe aka markado shi tun baje ko ina ba kuma bashida laifin komai hasali ma ranan akiyama zai samu mahaifiyar sa yace me na miki kika kashe ni? Ya ke mama na me na miki kika kashe ni?
Kina tunanin duk sallan ki da azumin ki da sadakan ki da aikin hajjin ki idan ma kin yi me kyau ankarba kenan. Kina tunanin ko ran da Allah ya baki zaki iya biya da shi ne? Amma Allah baice ki biyasa ba yace Abu daya yake nema a wajenki duk umarnin da ya baki kibi Wanda ya hana ki ki hanu? Kawai ki bauta masa shikenan. Ke a tunaninki bautan ki ne zai kaiki aljanna? Aljanna fa kyauta fa zamuje Dan ko manzon Allah yace ba wai aikin sa bane zai kaishi Rahman Allah ne. Allah zai duba yaga ni how sincere are you in kinyi iya kokarin ki sai ya baki aljannah. Kuma idan mutum yayi iya kokarin sa ya sani in baiyi ba ma ya sani. Amma saboda ke asara bakibi Allan ba a haka bai isheki ba sai kin Saba mai kuma in anjima ance allah ya bamu aljanna kinfi kowa bakin cewa ameen. Ki kalli kanki da kayu ki kalli rayuwan ki yayi kama da na matan annabi? Su Kike kwaikwaya? Zasu saka irin kayan da kike sawa? Zasu kula maza yanda kike kulawa? Au basa jin waka kenan? Basu kalli arewa 24 ba. Toh have another look at your self dinkin kayan ki irin na yan film kike yi ko ba irin na yan film ba? Make up irin na turawa ne ko ba nasu ba ? Bikin auren da kuke yi yayi muku kama da yanda akayi auren manzo, sahabbai da mutanen kwarai? Kina tunanin sayid na Umar yaje dinnern sayidna Abubakar? Au duk basu je ba ? Sai kika kwaikwayo al'adan yahudawa kika kawo cikin musulunci bayan annabi yace duk Wanda kake so kana tare dasu. In annabi kike so toh muga kina kwaikwayon matan shi in kuwa maryam yahaya da something izzar so ne toh Allah ya raka taki gona kin dai San ruwa basa gamuwa da wuta. Yanzu ke da ace mahaifiyar ki yanda kike rayuwar nan taki haka ta rayu zakiyi alfahari da ita? Au bazakiyi ba? Akwai kura kenan? Toh ki gyara mana. Duk yayin nan Wanda suka kawo shi in yau akace za'a kaiki wuta kina tunanin zakuce a hada dasu ne? Ko raka ki kofar gate bazasuyi ba. Ke ko mahaifiyar ki bazata waiwaye ki ba duk yadda kuke da kusan ci da ita toh me yasa zaku bada lahirar ki akan wasu banzaye kunun bayan ludayi Karan kada miya? Ki danyi nazari mana duk samarin ana da suke miki zakin baki you look beautiful, hot, lovely wa ya mutu wa ya tashi in aka watsa miki acid kina tunanin zasu zauna? Ko kawayen ki watsewa zasuyi. Yanzu yanda yan Mata ke rayuwa idan yar shekara 50 tayi haushin ta za'ayi ayi Mata ca ana cewa ta zubda mutunci amma in akaji tsohuwa yar shekara hamsin tana bazo karatun Qur'ani kamar budurwa burge mutane zatayi. Wannan zai nuna miki Abu mai kyau na tarbiyya ba ruwan shi da shekaru Dan haka Wanda zaice miki AI yamzu lokacin ku ne wallahi kiyi saurin guje masa kuma ki tuna duj yadda kika yi nisa wajen sabon Allah in dai kina numfashi akwai AI dama karshen matsala in kika ji kasa a kanki. Ki koma ga rabbal alamin Wanda ke ciyar da me bauta masa da mara bauta masa ya bawa Arne kudi ya bawa musulmi kudi. Rayuwar ki da kika gani jarabawa ce shaidan yayi ba gaida ba dalili kawai Dan allah yana son yan Adam kishi tasa ya dauki tsana ya daura mana amma saboda ke ba Wanda ya kaiki karamar kwakwalwa sai kuma ki dinga daukan shawaran babban makiyinki bayan kinsan makiyin ki ne kuma ya fito karara ya fada miki bazai bari ki zauna lafiya ba kwanciyar hankalin sa daya ya ganki a wuta. In kuka hadu a wutan ma kuna cewa shi yaja muku zaice bai miki dole ba "kad da'autukum fastajabtum li" kawai kiran ku yayi kuka amsa yace ina masu son zuwa wuta ku kuma kuka ce gaku. Shiyasa run yanzu ko wace yarinya ta bude idon ta Allah yace 'I'ilam annamal hayatad duniya la'ibun wa lahwun wa zeenah" its rayuwar duniya wasa ce toh ke Allah yace miki wasa ce sai ki dauke ta da gaske har ki sadakar da gaskiya saboda wasa yanzu sai ki rusa mansion dinku saboda gidan kwali ko gidan kara ? Kiyi tunanifa.
Share to save your sisters please
✍🏻Miss untichlobanty 💕