AYI AMFANI DA DAMA KAFIN TA KUFCE



AYI AMFANI DA DAMA KAFIN TA KUFCE

Da yawan Samari mugun kwadayi gare su, su kuma yan matan Dogon burin tsiya, duk sai ka rasa wane irin tunani ne muke da shi.

 Shawarata gare ku itace: Ku auri waɗanda kuka yaba da Addininsu da kuma halayyar su, sbd da yawa ba Kowa ne ke aurar abinda zuciyarsa ke muradi ba a farko, amma sai bayan auren ne yau da gobe ke tabbatar musu da gaskiyar lamarin itace mace kuma abokiyar zama tagari ko shine miji nagari, duk.dai daga baya suke gane ashe su ne mafi Alkhairi gare su ba waɗanda tunaninsu ke tinato musu ba
😍

Amma muddin kika tsaya lissafin irin kalar mijin da kike dakom zuwansa Lallaikam za ki bushe a tsaye, kuma ba lallai ne zuwansa ba tunda ba alkawari kukayi da ALLAH zai kawo miki shi ba, kuma akarshe kiyi da kinsanin da ba ta da amfani.

Kai ma muddin ka tsaya jiran yin auren Jaari ko mace mai irin launin da ba a cika samunsu a garinku ko a kasarku ba,na tabbata za ka iya yin da na sanin da ba ta da amfani.

Shi lokaci ribatarsa akeyi idan har ya kufce shikenan kuma anyi asararsa kenan ta yadda dawowarsa ba lallai ba.

ALLAH yayiwa rayuwarmu albarka, kuma ya aurar da masu shirin aure Saboda tsare mutuncinsu da Addininsu, kuma ya shiryi masu burace-burace mara ma'ana kuma ya aurar da su ga waɗanda suka fi alkhairi gare su.

✍🏻 Idris M Rismawy Abu Nu'aym
Post a Comment (0)