_*KA BA NI DON ALFARMAR ANNABI !!*_
https://chat.whatsapp.com/Cnf26Q8MPqz9yUYU1nxqRq
*TAMBAYA*❓
Assalamu Alaikum Dr.
Malam wanda suke cewa ku ba ni don alfarmar
manzon Allah suma be kamata su dinga fadi ba?
*AMSA*👇
Wa alaikum assalam Akwai sabanin malamai akan
haka, amma mafi yawan malamai suna ganin ana
neman tsani ne da abubuwa uku kacal:
*1.* Ayyuka nagari, kamar ya ce: ka ba ni da son
Annabi.
*2.* Neman tsani da Allah ko daya daga cikin
siffofinsa.
*3.* Addu'ar mutumin kirki.
Wadannan abubuwa guda uku su ne ingantattun
nassoshi suka tabbatar ana neman tsani da su.
Wanda ya nemi tsani da alfarmar Annabi ba za'a ce
ya yi shirka ba, sannan bidiantar da shi yana da
wahala saboda akwai riwaya daga Imamu Ahmad
wacce take halatta fadin hakan, kamar yadda Sheik
Sa'ady Wanda ya rasu a (1393) ya ambata a
littafinsa Majmu'ul Fawa'id.
_*Allah ne mafi sani*_
_*DR. JAMILU YUSUF ZAREWA*_
Zaku iya samu wannan group na Facebook ta wannan hanyar👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Join us on Facebook🖕