BA'A KARANTA ALQUR'ANI A RUKU'U DA SUJUDA, SAI DAI ABINDA YAKE NA ADDU'A, ANA IYA KARANTASHI A SUJADA KADAI



BA'A KARANTA ALQUR'ANI A RUKU'U DA SUJUDA, SAI DAI ABINDA YAKE NA ADDU'A, ANA IYA KARANTASHI A SUJADA KADAI

https://chat.whatsapp.com/KeXayNmsBie671pMAKT9xN

*TAMBAYA*❓

Assalamu alaikum barka d asuba dan ina da tambaya mutum yake bukatar wani abu agurin Allah sai kaceyarinka karanta wanna addu,a asujjada ومن يتق الله يخعل له مجرخا ومن يتوكل على الله و فهوحسبه ان الله بلغ امره قدجعل الله لكل شىء قدرا abin nufi anan shine an tsallake ويرزقه من حيس لايحتسب shin yahalitta 
Pls Dan Allah ina jiran ammasa


 *AMSA*👇

Wa alaikumus salamu wa rahmatullahi wa barakatuh. Alhamdu lillahi rabbil alamin wassalatu wassalamu ala rasulillahi wa ala alihi wa sahbihi ajma'in.

Tabbas hakan bid'ah ne, ya saba ma koyarwar Annabi ﷺ . 

Bayan haka an cire wani bangare na ayar don wani dalili da baya da goyon baya a shara'a. Sannan ko da a kaddara ba'a cire komai ba daga ayar, an kawo ayar cikakkiyar ta, Allah ya hana Annabi ﷺ karanta alqur'ani a cikin ruku'u da sujada, kuma Annabi ya hana mu karanta alqur'ani a cikin su, inda yace:

2746 - 1271 - «.... وإني نهيت أن أقرأ القرآن راكعا أو ساجدا فأما الركوع فعظموا فيه الرب وأما السجود فاجتهدوا في الدعاء فقمن أن يستجاب لكم» .
(صحيح) ... [حم م د ن هـ] عن ابن عباس. الإرواء 2539.

Annabi ﷺ yace muyi addu'a a cikin sujada, wannan aya kuma ba Addu'a bace, ko sabani babu tsakanin Mallamai cewa jumla insha'iyya ce, sun tafi a kan jumla ce khabariyya.

Don haka ba'a karanta alqur'ani a ruku'u da sujada, sai dai abinda yake na Addu'a, kamar *"rabbana aatina fid dunya hasanatan wa fil aakhirati hasanatan wa qina azhaban naar"* da makamantan ta, ana iya karanta su a sujada kadai.

Wallahu ta'ala a'lam.

 *_Amsawa_* :

 *Malam Aliyu Abubakar Masanawa*

Zaku iya samu wannan group na Facebook ta wannan hanyar👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Join us on Facebook🖕
Post a Comment (0)