IN KIN AIKATA KAZA A BAKIN AURENKI, SAI TA AIKATA
TAMBAYA❓
Assalamu alaikum. Malam mijina ya ce in na sake hawa Babur a bakacin aurena, to sai muka je kauyen da babu abun hawa sai Babur ga shi inda za mu je da bala'in nisa malam sai na hau babur din, ya matsayin aurena yake?
*AMSA*👇
Wa'alaikumus salam, idan miji ya ce wa matarsa idan kika aikata abu kaza a bakin aurenki, amma sai ya kasance manufarsa tsoratar da ita ce da hana ta aikata wannan abun, ba wai manufarsa sakinta ya yi ba, to abin da yake daidai daga tabbatattu daga cikin ma'abota ilimi shi ne: lallai hukuncin wannan shi ne hukuncin rantsuwa, zai yi kaffarar rantsuwa idan ta aikata wannan abin da ya hanata, amma idan ba ta aikata wannan abin ba babu komai a kansa, sai dai duk lokacin da ta saɓa masa ta aikata, to haqiqa ta yi kuskure, kuma ta saɓa, sannan zai yi kaffarar rantsuwa matuqar ta aikata wannan abin. Inji Allama Abdul'aziz Bin Baaz.
Duba Majmu'u Fatáwá Ibn Baaz (22/106).
Amma fa idan mutum ya faɗi cewa idan matarsa ta aikata abu kaza ya sake ta da nufin saki ɗin, sai kuma ta aikata ɗin, to wannan da ijma'in malamai saki ya tabbata, babu maganar daga baya ya ce ba saki yake nufi ba, tun da har ya furta saki, kuma ya nufaci hakan, Allah ya san duk abin da ke cikin zukatan mutane, in ma an ɓoye an qi faɗin gaskiya Allah ya sani, kuma zai yi hukunci a kai.
Don haka, yanzu za ki sanar da shi mijinki wannan al'amari ne, idan lokacin da ya faɗi maganar yana nufin ya sake ki ne, to saki ya tabbata, idan kuma ya faɗi ne da nufin ya tsoratar da ke, da hana ki hawa babur, to hukuncin wannan shi ne yin kaffarar rantsuwa kamar yadda wasu malaman suka faɗa, amma dai a ji tsoron Allah a yi aiki da abin da shi aka nufata tun farko!
Allah ne mafi sani.
Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.
Ga ma su sha'awar shiga wannan group sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu ta WhatsApp
08087788208
08054836621
Group Admin: 👇
MAL. HAMISU IBN YUSUF