▫️YAN MATA DA ZAWARAWAN KUMA DA NA KU GUDUMMAWAR WAJEN ƁARNA▫️
👉🏼 A yau an wayi gari duk wata mace budurwa ko bazawara wai ita a dole sai ta sanya sutura na yayi ta rike waya ta yayi, ta kuma ci abincin da a gidan su ba'a yi, kuma iri iri duk wanda aka fitar sabo na yayi dole ita ma ko ta wanne hali sai ta samu.
👉🏼 Shiyasa ɓarna yayi yawa maza kuwa akashi 70/100 ba su kashewa mace kuɗi face suna aikata wani abu na saɓon ALLAH da ita, ko sun tabbatar da za su aure ta ta zamo ta su, kwadayin canja waya da sanya suturu da dole sai anci me daɗi hakan ya sanya maza da dama lalata yanmata ko maida zawarawa karuwai.
👉🏼 Cikin sutura da matan yanzu ke sanya tsirara suke tafiya kuma ALLAH da manzon sa (saw) sun tsinewa masu sanya irin wannan sutura, bayan haka social media ɗaura hotuna ana rawa, hotunan tsiraici da sauran su, in namiji ya ga mace a hanya duk sai yaji sha'awar ta yake haka a social media su basu sani ba dayawan wasu hotunan su maza na banza na amfani da su sosai, shiyasa kuma yanzu soyayya ta sha'awa ysyi yawa namiji yaga mace yana so maimakon ta kara neman soyayyar sa ta hanyar kyautata wa da tarbiyya da soyayya yadda bai saɓawa Shari'a ba, a'a sai ta fara sanya turare mai kamshi in yazo hira da kuma sutura mai nuna tsiraici irin wannan al'amuran dayawa shi ya sanya masoya dayawa fadawa sabon ALLAH saboda dukkan su lallai sun kai matsayin jin bukatar juna domin su ba itace bane.
👉🏼 Hakan ya sanya maza da dama jin ba sai sun kara aure ba su a yanzu ga yanmata zawarawa na tura musu hotunan tsiraici da kuma yarda su kwanta da su ko taɓa jikin su a yan kuɗi kadan ko abu kaɗan kamar waya, abun ci da sauran abubuwa, shine sai kaji mace na cewa mijina ba ya ban hakki na na aure se chat da daddare, yadda lamari yake duk ya gama lalatar sa a waje ya ma dawo gidan yana ta CHATTING da wasu yanmatan na shi, gobe kuma da waccece za'a haɗu? .
👉🏼 Kuna ta kukan rashin miji yanmata zawarawa? Kowa yazo sai Maganar banza eh mana suturar ki ta banza kwaɗayi yayi yawa, majority mata kuma sunfi son mai taɓa su, hakan ya sanya har wasu mazan kirki da ba sa yi suka fara yi, saboda in baka taɓa ba to wallahi gaye za ta samu shi boyfriend na shan minti, ku jajirce matuƙa duk wanda yazo neman ku kada ku taɓa aminta ya taɓa ku, ku gyara suturun ku kuna shigen kirki na addini, ku cire kwaɗayi kada ku yarda kuyi soyayya da namiji wai babu izinin iyayen ku, ku jajirce dik son da kike wa namiji kada ki yarda kiji ko kamshin sa bare ya rude ki amma matukar wallahi ba ku daina ba, to fa mazajen aure kam kullum kara karanci za su yi ta yi, idan kina da wani da kike wannan alaka dashi na sabon ALLAH ki tuba ki daina, ki natsu amma yau saboda barna yadda yayi yawa ko mace na kirki ba ta tsallake wa zargi ba.
👉🏼 Ku kuma matan aure wani lokacin da na ku matsalar sai ku hana miji aure ko kullum yayi kuna bi ta boka malam kisisina makirci ku hana matar zama to ku natsu, Shiyasa maza dayawa yanzu suna yin permanent macen banza a waje saboda kuma ke kin hana mishi aure, kuma yana kashe mata dukiyar da ba ya kashe miki, wannan kuma abun kunya ne har gare ki da ya'yan ki, kisani lallai ke abun tambaya ne idan kuma kika zamo sanadiyyar saɓon ALLAH kema kina da zunubi.
👉🏼 Maza aji tsoron ALLAH kada ka nemi yar mutane sai ka shirya wa aure, kada ka taɓa ta, idan tana wani hali mara kyau ka yi mata magana ta gyara, zina Babban laifi ne matuƙa ALLAH yace kada a kusance ta maza aji tsoron ALLAH, maza da dama kuma yau sai addu'a ko budurwa aka ga mai kamun kai mai tarbiyya har haɗa baki kuke wai wani yayi soyayya da ita yayi matukar makirci har ya taka ta maza kuma kuna da damuwa ina ruwan ka da ustazancin ta? Ba ga mata irin ka ba? ALLAH ya kyauta
👉🏼 Yanmata zawarawa matukar kuna so ku auru kuma ku gama da duniya Lafiya to kuji tsoron ALLAH ku koma tarbiyyar addinin Musulunci, ba shige na nuna tsiraici da rike waya da shafa mai bane ke kawo miji ko miji mai dukiya, a'a indai wa'ennan abubuwan ne sai dai ya janyo miki abokin zina, kiyi hakuri da abincin gidan ku waya ki rike daidai yadda ALLAH ya baki, ki auri wanda ALLAH ya aiko miki ki rufawa kanki asiri, ki kame kanki daga zuwa yawon shan ice cream ko bikin birthday, ko casu, abun dayawa ALLAH dai ya shirya mana zuriya iyaye yayyu kanne sai ayi ta addu'a.
Iyaye mata kuma da na ku gudummawar sosai, domin wani abun tabbas kunsan ya'yan ku na aikatawa amma wasu da yake ya'yan na ba su kuɗi baruwan su, domin a matsayin ki uwa wallahi duk wata motsin yarki dole ki lura ki kuma sani, duk da yaran yanzu shu'umai ne, da kinga sauyin tarbiyya ko wani abu kisanar da mahaifin ta ku dau mataki, ubanni maza ma sai a hankali duk dai yanzu rayuwa abar tsoro sai wanda ya kama hanyar shiriya yake addu'a kuma ALLAH kuma ya tseratar.
Rasheedah Bintul Islam.