MU KIYAYE YI WA YARA BAKI
👉🏻👉🏻Ko kunsa cewar duk abun da kuka furta ma 'ya'yan ku mai kyau ko marar kyau yana tabbata akan su ?
👉🏻Na taba jin labarin wata mata da danta yana qarami ya fasa mata kwanon tangaran cikin fushi tace yadda ka tarwatsa shi kaima sai ka tarwatse. Sai bayan shekaru dayawa yaron ya girma yayi karatu yana shirin aure yana ta gini sai yaje wurin ginin yana dubawa kawai sai bango ya fado mashi gaba daya yayi rugu rugu babu inda bai karye ba a jikin shi. Mahaifiyar shi tana bacci tayi mafarkin cewar tashi yau Allah ya amsa adduar ki nan take ta farka sai ga gawar danta an kawo mata ta tuna da maganar ta tun yara yaro.
👉🏻Iyaye mu kula da kalmomin da muke fadi ma yaran mu kamar su
1️⃣baza ka ga dai dai ba.
2️⃣Baza ka taba ci gaba ba.
3️⃣Rayuwar ka baza tayi kyau ba,
4️⃣ka dinga ganin matsala kenan,
5️⃣ko dan iska ko yar iska
6️⃣ko yarinyar banza ko yaron banza da dai sauran su.
👉🏻Duk yadda rai ya baci muyi qoqari wajen furuci mai kyau
👉🏻Wata uwa daga cikin magabata ta kasance da danta marar jin magana sosai amman duk lokacin da yayi mata ba dai dai ba sai tace Allah yasa ka zama *limanin* *makka* kuma fa ba a garin makka suke ba amman dai sai da Allah ya amsa mata adduar ta
👉🏻Fushin iyaye yana tare da fushin ubangiji haka kuma yarda iyaye na tare da yardar ubangiji.
👉🏻Fushin iyaye ba tare da furuci ba yana lalata yaro ballanta uwa ko uba sun furta kalma mai muni akan 'ya'yan su
👉🏻 Duk iyaye ba zasu so dansu ko yarsu su lalace ba ko rayuwar su ta qi kyau
👉🏻saboda haka Duk yadda yaran ki ko yaran ka duka bata maka kayi qokarin wajen furta cewar *Allah ya shiryar da ku. Allah yasa ku zama mutanan kirki. Allah ya ganar da ku gaskiya da dai sauran su*
👉🏻Allah ya shirya mana zuriya baki daya ya bamu ikon yi masu tarbiya mai kyau yasa su zama sanyin idaniya a garemu AMIN🤲🏻🤲🏻
Tura ma yan uwa don suma su amfana. Allah ina tawassali da wannan tunatarwar Allah ka shirya mana zuriya baki daya Amin🤲🏻🤲🏻🤲🏻