TA WACCE HANYA CE MUTUM ZAI IYA CIN GADON MACEN DA YA SAKA?


*TA WACCE HANYA CE MUTUM ZAI IYA CIN GADON MACEN DA YA SAKA?*

https://chat.whatsapp.com/Cnf26Q8MPqz9yUYU1nxqRq

*TAMBAYA*❓

Assalamualaikum Allah yagafarta malam tambayana shine Ance idan mace tamutu batada yara mijinta zai dauki kashi 1 bisa 4 idan kuma Tamara yara za.abashi 1 bisa 8 na abinda ta mallaka shin mijin dasuke tare dashi basu haihuba amma tanada yara awani gidan idan atashi rabon gadon za.bashi


 *AMSA*👇

Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuh. Alhamdu lillahi rabbil alamin wassalatu wassalamu ala rasulillah wa ala alihi wa sahbihi ajma'in.

Eh, ana baiwa mijin da matar sa ta mutu a ƙarƙashin igiyar auren shi ne, shi ke da gadon ta a lokacin da mutu suna aure tsakanin su, ba mutumin da ya sake ta ko suka rabu da shi ba har tayi idda ta gama ba.

Ana baiwa mijin da mace ta rabu da shi gado ne, idan sun rabu da sakin kome tsakanin su, É—aya ko biyu ke nan, kafin ta cika iddar ta. Duk wanda ya mutu a cikin su, a lokacin za su ci gadon juna. Amma idan har idda ta cika, toh babu gado tsakanin su, haka kuma idan saki na uku ne, a nan ma babu gado. 

Wallahu ta'aala a'lam.

 *_Amsawa_* :

 *Malam Aliyu Abubakar Masanawa*

Zaku iya samu wannan group na Facebook ta wannan hanyar👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Join us on Facebook🖕
Post a Comment (0)