*WASA DA FARJI DA YATSA, NONO, KO AMFANI DA WASU ABUBUWAN BIYAN BUKATA KAMAR SU; CANDLE, DILDO ETC*
Amfani da gaba dayan wadannan abubuwan dake a sama haramun ne.
Dalili kuwa shine dukansu istamna'i ne wato mutum yai wasa da gabansa har maniyyi yafita mace ko namiji. Biyan bukata ba tare da mata ko miji ko kuyanga ba kenan.
Wanda kuma haramunne a alqur'ani da hadisi. Ibnu kaseer rahimahullah yace : Imamu shafi'i da wadanda suka goyi bayansa yakafa hujja da haramcin wasa da gaba da fadin Allah madaukakin sarki.
(والذين هم لفروجهم حافظون إلا على أزواجهم أو ما ملكت أيمانهم فإنهم غير ملومين فمن ابتغى ورآء ذلك فأولئك هم العادون.
Muminai sune wadanda dangane dafarjinsu suke kiyayeshi, sai ga matayensu ko kuyanginsu dan basu kiyaye farjinsu akansu ba, su ba'ababen zargi bane, duk wanda yanemi wata hanya bata aure ba kota kuyangarsa wannan mai ketara dokokin Allah ne.
Imamu shafi'i acikin littafin Aure yace saiya kasance Allah yabayyana kiyaye farjinsu saifa akan matayensu ko abinda damarsu tamallaka, sai yazama haramun idan ba matar ka bace ko kuyangarka sai Allah ya karfafi maganar dacewa " wanda ya nemi koma bayan hakan yana cikin masu taka dokokin Allah"
Bai halatta amfani da azzakari ba sai akan matarka baiwarka, bai halatta jindadi dashi da hannu ba wallahu A'alamu kitabul ummu na imamu shafi'i.
Wasu malaman sun kafa hujja taharamcin istimna'i da fadin Allah madaukakin sarki
(وليستعفف الذين لا يجدون نكاحا حتى يغنيهم الله من فضله سورة النور 33
Wadanda basu samu damar aure ba sukame harsai Allah ya wadata su daka falalarsa.
Sukace: umarni da kamewa yana nuna hakuri da rashin samun yin auren ko kuyangar.
A sunnah kuwa sunkafa hujja da hadisin Abdullahi dan mas'ud Yardar Allah takara tabbata agareshi yace: Munkasance tare da Annabi sallallahu Alaihi wasallam muna samari bamu samu komai ba sai Annabi sallallahu Alaihi wasallam yace damu "ya ku taran samari duk wanda yasamu halin daukar dawainiyar iyali yayi aure, domin ya nasa kamewa daka gani, yana kuma tsare farji, wanda kuma bai samu dama ba to nahore shi dayin azumi domin azumi yana kariya daka fadawa haram. Bukhari 5066.
Sai shari'a ta shiryar lokacin da mutum yagajiya wajen yin aure saiya dunga azumi tare da wahalarsa, shari'a bata shiryar zuwa wasa da farji ba, tare da saukinsa akan azumi tare dahaka ba'a halatta shiba.
*YADDA MUTUM ZAI MAGANCE WANNAN DABI'A SUNE KAMAR HAKA*
1-Wajibine mutum yakubutar dakansa daka wannan al'ada dan nisantar abunda Allah ya haramta da kwatanta bin umarninsa da gujewa fushin sa. Yan mata ku daina irin chating dinnan da samari musamman irin wanda ke motsarda sha'awa tsakaninku.
2-kawar da wannan da lafiyar jiki shine aure saboda wasiyyar manzan Allah sallallahu Alaihi wasallam ga samari.
3-Kawar da hadurra da waswasi da zuciya zata dunga sakawa, da shagalta datunani cikin abunda zai amfaneka duniya da lahira, domin yawan waswasi datunani yanakai mutum zuwa ga aikata abu, sannan mutum yasaba tayanda zai masa wahalar gasken gaske wajen kubuta daka aikata shi .
4-Kamewa daka gane gane domin kallace kallacen wasu abubuwa da hotuna nazane damasu motsi rayayyu ko matattu yana kai mutum zuwa haram.
5-Shagaltuwa da ibadoji kala kala dakin barin sarari ga aikin sabo.
6-Izna da cutukan dake haifarwa jiki na raunin gani da gabbai da ciwan baya da sauransu.
7-Riko da maganin manzan Allah sallallahu Alaihi wasallam shine azumi.
8-Lazimtar ladubban shari'a yayin bacci na karanta zikirori
9-Kaskantar dakai ga Allah daneman taimakonsa.
10-Gaggauta tuba da istigfari da aikata ayyuka na gari, tare da rashin debe tsammani daka Allah.
11- Mutum ya nisanci kwana kai kadai adaki domin Annabi sallallahu Alaihi wasallam yahana mutum yakwana adaki shi kadai.
Sa'annan maganar cewa kiyi wasa da hannu domin gujewa sabawa Allah to ai shima wannan sabawa Allah ne. Saboda haka yar uwa ba wata hujja da zaki dinga amfani da hannunki ko wani sashe na jikinki domin ki biya bukatarki. Abinda zaki yi shine kibi hanyar da shari'ah ta tanadar in shaa Allahu zaki samu waraka, hanyar kuma itace wadancan shawarwarin dake a sama musamman wadannan:
~ Idan kina chating da samari mai motsa sha'awa kiji tsoron Allah ki daina.
~Ki yawaita yin azumi
~Ki daina kallon hotunan batsa ko hirar batsa da maza ko mata yan uwanki
~Uwa uba kuma shine ki sanarda iyayenki kefa aure kike so ayi miki aure ki huta. Nasan yanzu haka kina da samari masu sonki sai ki ba daya dama ya turo iyayensa. Kinga shikenan an huta. Allah ya qara kare mu.
والله أعلم،
***********************************
سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا انت أستغفرك وأتوب إليك.
_*🌙Tambayoyin*_ _*Musulunci🌙*_
_*WhatsApp*_ _*Group*_
_*🎙ZAUREN SAWTUL HIKMAH 🎙 (da'awar sunnah a social Media's) 🌎*_
*• Ga masu buqatar shiga Zauren Sawtul hikmah zasu iya bi ta links din da ke ƙasa👇*
https://t.me/sawtulhikma
https://www.facebook.com/sawtulhikmah
https://t.me/sawtul_hikmah
https://twitter.com/sawtulhikmah01
*🎙️SAWTUL HIKMAH TAKU CE DOMIN YAƊA SUNNA💪*