Wasu kiristoci ne guda biyu suka bata a sahara. Suna can lalube ga yunwa ta damesu sai suka hango wani masallaci a tsakiyar hanya. Suna ganowa sai dayan ya ce ai kawai zuwa za su yi su nemi alfarma ta hanyar cewa su musulmai ne. Dayan ya ce shi ba zai yi karya ba.
Suka dauki hanya suka tafi bakin masalllacin nan. Aka karbesu aka tambayi sunansu. Wanda ya ce zai ce shi musulmi ne ya ce sunan Mas’ud. Shi kuma wanda ya ce ba zai karya ba ya ce sunansa Alex. Ai kam sai aka kawo abinci aka bawa Alex shi kuma Mas’ud aka tuna masa cewa a watan Ramadan ake.
A dena karya jama’a 🤣🤣🤣