BABU MAI YIN HAKA SAI MUTUMIN KIRKI



BABU MAI YIN HAKA SAI MUTUMIN KIRKI

YIN ADDU'A GA MAHAIFA AIKINE NA MUTANEN KIRKI

An tambayi daya daga cikin magabata wannan tambaya,wani daga cikin Dalibansa ya ce dashi"):
*"Shin Malam ina cikin mutanai Salihai mutanan kirki??"*.

Sai ya amsa da cewa:
"Idan har kana yawaita yin addu'a ga Mahaifanka to hakika kana cikin Salihan bayi na kwarai,Saboda Hadisin da Annabi s.a.w yake cewa:
(Idan dan Adam ya mutm dukkan aiyukasa sun yanke"ma'ana ladar aiyukansa ta daina karuwa ko gudana" Sai abubuwa guda ukku:-
*Sadaka mai gudana*
(Kamar gina masallaci ko rigija ko islam ko hanya).
*Ko wani ilimi da ka koyar*
*Ko wani yaro salihi na kwarai da zai riqa yi maka addua)*.
@Saheehul Jami'i.

Sai Annabi s.a.w ya tabbatar mana anan cewa yana cikin babbar alamar salihin mutum ya kasance yana yiwa mahaifansa addua ako wane lokaci.

Idan kuma bakayi masu addua to kai ba mutumin kirki bane,iya yadda ka manta da yiwa mahaifanka addua iya yadda kake zama mutum banza.

Dan haka ka yawaita fadar:
( رَّبِّ ارْØ­َÙ…ْÙ‡ُÙ…َا ÙƒَÙ…َا رَبَّÙŠَانِÙŠ صَغِيرًا )
*"Ya Ubangijina! Ka yi musu rahama, kamar yadda suka yi rẽnõna,ina ƙarami."*

Wannan addu'ar ta kunshi abubuwa guda biyu da akeso mu yawaita yima mahaifan mu.

*1-Nema masu gafara*
*2-Da nema masu Rahama da kuma kyautata masu*
*3-Nema masu aljanna da nema masu tsari daga wuta da Azabar qabari*.

Ya Kayi rahama da jin kai da gafara ga mahaifan mu baki daya.

رَّبِّ ارْØ­َÙ…ْÙ‡ُÙ…َا ÙƒَÙ…َا رَبَّÙŠَانِÙŠ صَغِيرًا .
Post a Comment (0)