DAGA CIKIN LADUBBAN KWANCIYA BACCI (01)
Bacci Wani Ɗabi'ace da Ubangiji Ya Sanyawa Halittunsa Domin Samun Hutu da Natsuwa Cikin Rayuwarsu ta Yau da Kullun. Ubangiji Maɗaukaki Yana Cewa a Cikin Littafinsa Mai Girma:
(وَجَعَلْنَا نَوْمَكُمْ سُبَاتًا)
“Kuma Muka Sanya Barcinku Ya Zamo Hutu a Gareku".
Ubangiji Ya Sanya Bacci Ya Zamo Hutu Ga Halittunsa Yayin da Sukayi Aiki Suka Gaji, Don Sake Samun Natsuwa da Karsashin Bauta ga Ubangiji.
Bacci Yanada Ladubba da Addinin Musulunci Ya Shimfiɗa Wanda Duk Wanda Ya bisu Yayin Baccinsa Zai Zamo Tamkar Yana Ibadah Ne Saboda Lada Da Za'a Dinga Rubuta Masa Bayan Kariya da Zai Dinga Samu Daga Mala'iku Har Zuwa Lokacin da ya Farka. Ladubban Sun Haɗa da:
1. YIWA KAI HISABI GABANIN YIN BACCI: Anso Musulmi Ya Dingayiwa Kansa Hisabi a Duk Lokacin da Yazo Kwanciya Bacci Game da Abinda Ya Aikata a Wannan Yinin. Idan Yaga Abinda ya Aikata a Yinin Na Alkhairi Yafi Yawa Sai Ya Godewa Allah Ya Kuma Ɗaura Niyyar Ƙara Dagewa a Yini Mai Zuwa.
Idan Kuma Akasin Hakan Shine Ya Rinjayi Ayyukansa Na Alkhairi a Wannan Yinin, Sai Ya Nemi Gafarar Ubangiji Tare da Yin Gaggawan Tuba Zuwa Gareshi da Kuma Ɗaura Niyyar Ganin Yininsa Mai Zuwa Yafi Wanda Ya Wuce Zama Alkhairi.
Haƙiƙa Duk Wanda Zai Lizimci Yiwa Kansa Hisabi, Kafin Hisabin Lahira, Lallai Zai Samu Sauƙin Al'amura Yayin da Ya Haɗu da Ubangijinsa. Umar bn Khaɗɗab (ra) Yana Cewa:
(حاسبوا أنفسكم قبل أن تحاسبوا، وزنوها قبل أن توزنوا.....)
“Kuyiwa Kanku Hisabi Gabanin Ayi Muku, Ku Auna Ayyukanku Gabanin a Auna Muku.....".
2. KWANCIYA DA WURI: Mustahabbine Mutum Ya Kwanta Da Wuri Domin Samun Daman Tashi a Ƙarshen Dare Don Ganawa ga Mahalicci. Hadisi Ya Tabbata Manzon Allah (ﷺ) Yana Cewa:
(عن عائشة رضي الله عنها أنَّ رسول الله صلى الله عليه وسلم كان ينام في أول الليل ويقوم آخره فيصلِّي)
( متفق عليه )
“An Kar6o Daga Aisha (ra), Lallai Manzon Allah (ﷺ) Ya Kasance Yana Bacci a Farkon Dare, Sai Ya Farka a Ƙarshensa Yayi Sallah".
(Bukhari da Muslim)
Anan Zan Dakata Sai Mun Haɗu a Rubutu Na Gaba Insha Allah
سُبْحَانَكَ اللَّهُمَّ وَبِحَمْدِكَ، أَشْهَدُ أَنْ لا إِلَهَ إِلا أَنْتَ، أَسْتَغْفِرُكَ وَأَتُوبُ إِلَيْكَ
✍🏼Abu Aysha Al-Maliky
TELEGRAM:
https://t.me/joinchat/OOh5_RUljMIixFLQgNCDyg
