HUKUNCIN HADA SITTU SHAWWAL DA RAMUWAR RAMADAN



HUKUNCIN HADA SITTU SHAWWAL DA RAMUWAR RAMADAN


*Tambaya :*


Malam idan ana binka ramuwar azimi za ka iya niyya biyu : wato da nufin sittu shawwal da ramuwar Ramadhana a guda daya ? don Allah mlm taimaka min da bayani.

*Amsa :*


To ‘yar’uwa kowanne daban ake yinsa, saboda manufarsu ta banbanta, don haka ba za’a hada su da niyya daya ba, kamar yadda ake yi a wankan janaba da wankan juma’a, za mu fahimci haka, a cikin fadin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi :
“Duk wanda ya azumci Ramadhana sannan ya biyar da kwanaki shida na Shawwal, Allah zai ba shi ladan wanda ya yi azumin shekara”

Muslim ya rawaito shi a hadisi mai lamba ta : 1164, kin ga wannan yana nuna Ramadan daban, sittu-shawwal daban. Fadin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi :
” Sannan ya biyar da kwanaki shida na Shawwal” ya sa wasu malaman sun tafi akan cewa : bai halatta ayi sittu-shawwal ba, sai bayan an kammala ramuwar Ramadan. Kamar yadda ya zo a : sharhurmumti’i 6443
Allah ne ma fi sani

*Dr Jamilu zarewa*

05-05-2018

Daga 
*MIFTAHUL ILMI*

ZaKu iya Bibiyar Mu a 
Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml

Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi

WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248
Post a Comment (0)