TAYA NI GANI



TAYA NI GANI

Ita Mace, in tana shekaru 16-21, kamar kwallon kafa take kan farin jini, Mutum 22 a fili, kowa na so ya nuna bajintarsa don ya sami nasara. Ita kadai, suna ta rubibinta.

In Mace takai shekara 22-25 sai ta koma kamar Kallon kwando. Mutum goma ne ke gasar nuna bajinta akanta. Mai rabo ya samu.

Daga shekaru 26-30, sai ta koma kamar kwallon tebur. Mutum biyu ne ke fafatawa. Tsakaninsu wanda yayi nasara ba wata murnar kirki yake ba.

In shekarunta sun kai 31-35 kuwa, kamar kwallon Gora (golf) take komawa. Mutum ya buga a barsa, in ta fada rami ya dauko in ma ta wuce ya dauko. Shi yake fama shi ka dai ana kallonsa.

A nan, ne in abubuwa ba su tafi yadda ake so ba, sai ta koma yar kungiyar kare hakkin mata da yara. A shiga rediyo ana zagin mazaje ana hure kunnen matan da Allah Ya sa hakonsu ya cimma ruwa suke tsugune gidan mazajensu.

Yakamata a lura, yawancin maza dake zuga mata suna daukar kansu dai dai da maza a fagagen rayuwa ingiza mai kantu ruwa suke musu.

Mace ta gama shaharar da bololon su watsar da ita. Tana zaune dan cin fuska sai a miko mata ENGAGEMENT dinsa da wata yar sakandare. Ko mai kama da haka. Ita ko nata sai fatan alheri da sanya ido

Allah ya sa mu gane.

Rauwan
180519

Daga 
*MIFTAHUL ILMI*

ZaKu iya Bibiyar Mu a 
Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml

Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi

WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248
Post a Comment (0)