TARIHI MUDUBIN MU= 2
Map na tafiye-tafiyen Imamul Bukhari a neman Ilimin Hadisin Manzon Allah (saw)
Abu ne sananne babu abin da ya raba 'Yan Bidi'a da Ahlus Sunna sai neman ilimin Hadisan Manzon Allah (saw) da gaskata su da aiki da su da binsu sau da kafa. Wannan ya sa 'Yan Bidi'a tun zamanin da, har zuwa yau, hadi da makiya Addinin Muslunci cikin "Mustashriqoun" (Orientalists) da yaransu 'Yan Boko Aqida a kullum suke yakar Hadisan Annabi (saw), musamman littafin da ya fi kowanne inganci a cikinsu, wato Littafin "Sahihul Bukhari", na Imam Abu Abdillah, Muhammad bn Isma'il Al-Bukhariy.
Imamul Bukhariy babban Malamin Hadisi ne, har ya kai kololuwar daraja a ilimin Hadisi, inda ya cancanci lakabin "Amirul Muminina fil Hadeeth".
To kasancewar Sunna ita ce ruhin Muslunci da bayanin Alkur'ani, shi ya sa 'Yan Boko Aqida a kullum sara da sassakansu ya kare a kan "Sahihul Bukhariy", saboda in sun yi nasara sun cire kwarjininsa a zukatan Musulmai to shi kenan sun ci nasarar yakar Muslunci a zukatar Musulmai, wannan ya sa a kullum ba sa gajiya da sukar wannan babban littafin da har yau babu kamarsa cikin littatafan da bil'adama suka wallafa.
Imamul Bukhari ba karamar tafiya ya yi wajen neman ilimin Hadisin Annabi (saw) ba. Ya shafe tsawon 13900 KL a tafiya irin ta wancan lokaci, zamanin tafiya a kan doki da jaki da rakuma.
Duk garin da ya je sai ya zauna a garin, ya hadu da Malaman Hadisi da suke garin, ya dauki Hadisi a wajensu, ya rubuta ya haddace, kuma ya yi "Muzakara" (bita) tare da daliban Hadisi a garin, har ya yi wallafe-wallafe a wasu garuruwan, kamar yadda ya wallafa "Al-Tarikhul Kabeer" a birnin Madina.
Da farko ya taso daga garinsu Bukhara (birni da ke kasar Uzbekistan a yanzu) ya tafi garin Balkh (garin da ke cikin kasar Afghanistan a yanzu) tafiyar tsawon 599 KL.
Daga Balkh kuma ya wuce Merv (birni da ke kasar Turkmenistan a yanzu) tafiyar tsawon 792 KL.
Daga Merv kuma ya wuce Nishapur (birni da ke kasar Iran a yanzu) tafiyar tsawon 136 KL.
Daga Nishapur kuma ya wuce Rey (birni da ke kasar Iran a yanzu) tafiyar tsawon 757 KL.
Daga Rey kuma ya wuce Wasit (gari da ke kasar Iraq a yanzu) tafiyar tsawon 984 KL.
Daga Wasit kuma ya wuce Basra (birni da ke kasar Iraq a yanzu) tafiyar tsawon 364 KL.
Daga Basra kuma ya wuce Kufa (gari da ke kasar Iraq a yanzu) tafiyar tsawon 396 KL.
Daga Kufa kuma ya wuce Baghdad (babban birnin kasar Iraq a yanzu) tafiyar tsawon 164 KL.
Daga birnin Baghdad kuma ya wuce Medina (birnin Manzon Allah (saw) da yake kasar Saudi Arabia a yanzu) tafiyar tsawon 1524 KL.
Daga birnin Medina kuma ya wuce Mecca (birni mai alfarma da yake kasar Saudi Arabia a yanzu) tafiyar tsawon 432 KL.
Daga birnin Mecca kuma ya wuce Jeddah (birni da yake kasar Saudi Arabia a yanzu) tafiyar tsawon 70 KL.
Daga Jeddah kuma ya wuce ‘Aydhab (ruwa ya mamaye garin, yana tsakanin mallakar Egypt da Sudan) tafiyar tsawon kusan 130 KL.
Daga ‘Aydhab kuma ya wuce Fustat (gari da yake kasar Egypt a yanzu) tafiyar tsawon 1073 KL.
Daga Fustat kuma ya wuce Ashkelon (gari da yake kasar Israel a yanzu) tafiyar tsawon kusan 500 KL.
Daga Ashkelon kuma ya wuce Caesarea (gari da yake kasar Israel a yanzu) tafiyar tsawon 118 KL.
Daga Caesarea kuma ya wuce Damascus (babban birnin kasar Syria a yanzu) tafiyar tsawon kusan 400 KL.
Daga garin Damascus kuma ya koma Baghdad tafiyar tsawon 913 KL.
Daga Baghdad kuma sai ya kama hanyar da ya tafo har ya koma gida Bukhara.
Saboda haka wannan shi ne tafiye - tafiye da wannan bawon Allah ya yi don neman ilimin Hadisin Annabi (saw), ta hanyar rubutawa da haddacewa, da kuma tace ingantattu daga wadanda ba su inganta ba, har ya tara mana ingantattun ya wallafa mana "Al-Sahihul Jami'u", littafin da ya zama bakin ciki ga 'Yan Bidi'a da makiya Addinin Muslunci, cikin "Mustashriqoun" (Orientalists) da yaransu 'Yan Boko Aqida.
#Muhd Sani Umar
Daga
*MIFTAHUL ILMI*
ZaKu iya Bibiyar Mu a
Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml
Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi
WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248