*KAYI ADALCI KODA AKAN MAKIYINKANE*
Wassalatu wassalamu ala rasulillahi (s.a.w)
Tun bayan bullowar fitinar wadannan matasan wadanda suke badda'a manyan Malaman sunnah wadanda suke da'awar cewa babu sauran ahalus sunnah a najeriya face sukadai kuma suna cewa sudin 'yan salafiyyah ne wanda kuma duk me ilimi yasan cewa karya sukeyi su ba 'yan salafiyyah bane Haddadiyyah ne su.
Toh a hannu guda kuma se aka samu wasu mutane masu adawa da da'awar Sheikh Rabi'u Binu Hadi Almadkhali musamman dayake su din mafi yawansu sunadai da'awar sunnah kuma muma mun yarda sudin ahalus sunnah ne amma suna samun abinci da tallafi daga wajen kungiyar Muntada ta Sururiyyah kokuma suna Samu daga wajen Ikhwan kai tsaye wanda kuma duniyar ilimi a wannan zamanin tasani cewa Sheikh Rabi'u Almadkhali shine mutuminda yafallasa asirin Ikhwan da Sururiyya shine yabayyanama duniya wanene Hasnul Bannah jagoran 'yan Ikhwan kuma shine ya tona Asirin Sayyid Khudub Uban tafiyar Ikhwan sannan shine ya tona Asirin irinsu Safarul Hawani dasu Ã'idul Qarni harma da shi kansa Muhammad Surur Zainul Abidin wato wanda shine ya mallaki waccan kungiya ta Muntada wacce takeda hedkwata a birnin Landon na birtaniya kuma suna samun tallafine daga turawan birtaniya
Toh tun sadda aka samu bayyanan wadancan matasa wanda duk wanda Allah yasa yakeda wayewa ta addini kai kana kallon tsarin tafiyar matasancan kasani cewa da'awace ta Haddadiyya suke tallatawa domin su dama haddadiyya basuda kunyar su kalli babban malami komai kafuwarshi agidan ilimi sesuce masa dan bidi'a. Toh su wadannan Haddadiyyar suna karkashin wani Malami Muhammad Haddad Almisri shine jagoransu wanda abaya shima yataba zama dalubin Sheikh Rabi'u binu Hadi Almadkhali kafin sadda yasamu wannan fahimtar se dalubin da malamin sukayi baram baram.
Amma abun mamaki wai anan kasar sekaga Malami wanda ake ganinshi yanada hasken ilimi sekaji yace wai wadancan Matasan masu da'awar bidi'antarda Malam Jafar Adam dasu Albani Zaria sekaji yace wai 'yan Madakhilane wato yana jinginasu ga Sheikh Rabi'u Almadkhali bayan kuma Allah yasani Sheikh Rabi'u kokadan bashida irin wannan aqidar sedai dayake mafi yawan wadanda yatara agabanshi basusan wanenen Sheikh Rabi'unba da irin kafuwarsa agidan sunnah
Yanzu kuma idan da zakace Malam Jafar Adam Dan Boko Haramunne tunda Jagoran Boko Haram Muhammad Yusuf yataba zama almajirinsa, sesuce maka Aa aishi Malam Jafar kokadan bashida wannan aqidar kuma yayi inkari wa Muhammad Yusuf, kaga anan sun korewa Malam Jafar duk da cewa dalubinsane jagoran tafiyar, toh dan Allah meyasa shi Sheikh Rabi'u bazakuyi masa irin wannan adalcinba tunda kowa yasani cewa be taba goyon bayan tafiyar haddadiyyaba kuma yafito a idon duniya yayi baram baram dasu?? Idan zamu fadi magana muyi adalci koda akan makiyinmune
Amma yanzu bari inhaska muku maganganun manyan malamai na duniya kuji abunda suka fada akan Sheikh Rabi'u Almadkhali wanda ayau a kasarnan makiyansu suke jingina iskancin wadancan matasan zuwa gareshi
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
قال فضيلة الشيخ خالد بن ضحوي الظفيري
_حفظه الله_ : " سمعت بأذني الشيخ ابن باز رحمه الله يقول مخاطبا ربيع : ( يا شيخ ربيع رد على كل من يخطئ ، لو أخطأ ابن باز رد عليه ، لو أخطأ ابن إبراهيم رد عليه ...) وأثنى عليه ثناء عاطرا ، والله على ما أقول شهيد ".
*Sheikh Khalid bin Dahwi Azzafiry yana cewa: Da kunnena naji Sheikh Binbaz yana cema sheikh Rabi' (YAKAI SHEIKH RABI' KAYI MARTANI GA DUK WANI WANDA YA KAUCE HANYA, IDAN DA ACE IBNU BAZ ZE KAUCE HANYA TOH KAYI MASA RADDI, IDAN DA ACE IBNU IBRAHIM ZE KAUCE HANYA TOH KAIMASA RADDI...) kuma yayi yabo ga Sheikh Rabi' wani irin yabo me kamshi. Allah shine shaida gameda abunda na fadi*****
[[الملخص الجميل(م1/ ص56)]].
💢 وهنا يحث العلماء بالشيخ ربيع المدخلي
_حفظه الله تعالى_
*Anan zakuji irin yadda Malamai suke girmama Shekh Rabi' suke yabonsa*
(❶) ❍ قَـالَ العلّامــة بنُ بـازٍ رَحِمهُ الله :
《 الشيخ ربيع من خيرة أهل السنَّة والجماعة ، ومعروف أنَّه من أهل السنَّة ؛ ومعروف كتاباته ومقالاته »
*Sheikh Binbaz yace: Sheikh Rabi' yana daga cikin za6a66un ahalus sunnah na musamman, kuma abune sananne cewa shi ahalus sunnah ne, littafan sa da maganganunsa duk sanannune*****
[ شريط بعنوان ثناء العلماء على الشيخ ربيع ] .
(❷) ❍ قَـالَ العلّامــة الألْبَاني رَحِمهُ الله :
《 إنَّ حامل راية الجرح والتعديل اليوم في العصر الحاضر وبحقٍّ هو أخونا الدكتور ربيع ، والذين يردون عليه لا يردون عليه بعلم أبداً ، والعلم معه »
*Sheikh Nasirudden Albani yace: Tabbas wanda yake rike da tutar ilimin jarhu wat ta'adil ayanzu a wannan zamanin saboda ya cancanta shine dan uwanmu Dr Rabi'. Kuma duk wadanda sukema shekh Rabi'u raddi toh bafa da ilimi suke masa raddi ba har abada domin ilimin yana wajenshi****
[ شريط الموازنات بدعة العصر ] .
• وقال رحمه الله :《 فهؤلاء الذين ينتقدون الشيخين -كما ذكرنا ( يعني الشيخين مقبل الوادعي وربيع المدخلي )
إما جاهل فيُعلَّم ، وإما صاحب هوى فيُستعاذ بالله من شره ، ونطلب من الله عز وجل إما أن يهديه وإما أن يقصم ظهره 》
[ س.الهدى والنور (851) ] .
*Sheikh Albani yace: Wadanda sukeyin raddi ga Malamai biyu (wato yana nufin Muqbil Alwãdi'i da Sheikh Rabi Almadkhali) yace duk me sukar wadannan toh kodai shi jahili ne se a karantar dashi, kokuma dan bidi'ne shi se munemi tsarin Allah daga sharrinsa, semu roki Allah kodai ya shiryashi kokuma ya karyashi****
(❸) قال الشيخ العلامة محمد بن صالح العثيمين رحمه الله فيمن يطعن في الشيخ ربيع : «رأيُنا أنَّ هذا غلطٌ وخطأٌ عظيم، والشيخ ربيع من علماء السنة ، ومن أهل الخير ، وعقيدته سليمة ، ومنهجه قويم ، لكن لما كان يتكلم على بعض الرموز عند بعض الناس من المتأخرين وصموه بهذه العيوب »
[ شريط كشف اللثام ].
*Sheikh Usaimin yace: Wadanda suke sukar Sheikh Rabi': Aganinmu sunyi wauta kuma sunyi kuskure me girma, Amma Sheikh Rabi' yana daga cikin malaman sunnah, kuma yana cikin mutanen alheri, kuma aqidarsa mekyau ce, sannan manhajinsa yanada qarfi, sedai yayinda yakasance yana yin magana akan wasu sashen jigajigan mutane wadanda sukeda daraja a wajen wasu 'yan bana bakwai, toh shine suke muzantashi suke jifanshi da soke soke****
(❹) قال العلامة مقبل الوادعي -رحمه الله :
• وقال رحمه الله : « والشيخ ربيع بن هادي المدخلي فهو آيةٌ من آيات الله في معرفة الحزبيين »
[ تحفة القريب والمجيب ] .
*Sheikh Muqbil Alwãdi'i yace: Sheikh Rabi'u binu Hadi Almadkhali shi kansa wata ayace daga cikin ayoyin Allah gameda sanin kungiyoyin bidi'a****
(❺) قال العلامة محمد بن عبد الوهاب البَنَّا رحمه الله :
«أنا أقول : إنَّ ربيع هادي يحيى بن معين هذا الزمان »
[ الثناء البديع ] .
*Sheikh Muh'd binu Abdulwahhab Albanna yace: Nikam ina cewa: Lallai Sheikh Rabi' binu Hadi shine Yahya binu Ma'in na wannan zamanin***
• وقال رحمه الله : « فَأَنَا أَعرِفُ السَّلَفِيَّ وَغَيرَ السَّلَفِيِّ وَأنتُم كَذلِكَ وَنَحنُ نَستَدِلُّ عَلَى سَلَفِيَّةِ الإِنسَانِ وَاستِقَامَتِهِ فِي هذَا الزَّمَانِ بَل عِندَ الأَجَانِبِ بِحُبِّ رَبِيعٍ » .
[ مسائل العلامة محمد البَنَّا ] .
*Kuma yakara cewa: Ni nasan dan salafiyyah kuma nasan wanda ba dan salafiyyah ba, kuma kamar haka kunsani, amma mudin muna kafa hujja akan salafancin mutum dakuma istiqamarsa a wannan zamanin Aa tawani bangaren da Qaunar sheih Rabi' muke gane waye dan salafiyyah***
(➏) قال الشيخ العلامة أحمد بن يحيى النجمي رحمه الله :
« فالذي يطعن في الشيخ ربيع هذا دليلٌ على أنَّه مبتدع ، على أنَّه يحبِّذ المبتدعين ويلمِّع أصحاب البدع »
[ فتاوى عبر الهاتف (12) ] .
*Sheikh Ahmad binu Yahya Annajmi yace: Duk wani wanda yake sukar Sheikh Rabi' toh wannan hujjace akan cewa shi dan bidi'a ne, domin kuwa shi shekh Rabi' yana takurawa 'yan bidi'a yana matsama 'yan bidi'a***
(➐) قال العلامة زيد بن محمد المدخلي رَحِمهُ الله : « الردود التي قام بها الشيخ ربيع هي جهادٌ في إعلاء كلمة الحق وهي نصحٌ للمسلمين وبالأخص طلاب العلم المبتدئين ومن في حكمهم ممن ليس له عنايةٌ في التوسع في فن العقائد والمناهج والردود لئلا يقعوا في المحظورات والمحاذير » .
[ مقدمة كتاب (جماعة واحدة لا جماعات) ].
*Sheikh Zaid binu Mubammad Almadkhali yace: Irin raddodinda Sheikh Rabi' yakeyi toh hakan wani babban jihadine wajen daukaka kalmar gaskiya kuma raddin nashi nasihane ga musulmai musamman daluban ilimi masu fara karatu yanzu dama wadanda bada bada kulawa sosai akan aqida da manhaji, wadannan raddodin anayinsune dan kada mutane su auka cikin ababenda ake tsawatarwa****
(❽) قال العلامة عبيد بن عبد الله الجابري حفظه الله :
« إذا سمعتم من يطعن في عالمٍ من علماء السُّنَّة سواءً الشيخ ربيع أو غيره من العلماء المعروفين بالسُّنَّة والدعوة إليها ؛ فهذه علامةٌ على أنَّه مبتدع ٌ، فاضربوا صفحاً عنه وارفعوا أيديكم عنه وفاصِلوه »
*Sheikh Ubaid Aljãbiri yace: Idan kaji wani mutum yana sukan babban malami daga cikin manyan malaman sunnah duk dayane sheikh Rabi' ne ko waninsa daga cikin malamai wadanda aka sansu da sunnah da kira zuwa gareta, toh wannan alamace dake nuna shi dan bidi'a ne, ku kaurace masa kuma ku cire hannayenku daga gareshi kuyi watsi dashi****
-----------------
Toh menene yasa gashi manyan Malamai na duniya suna yabonshi amma kukuma anan kuna sukarshi? Anya kuwa baku sakaya lauje acikin nadi ba?? Wadancan matasan masu da'awar cewa Malam wane dan bidi'ane Malam Wane Dan bidi'ane toh mafi dacewa garesu shine ace musu 'yan haddadiyya wannan shine sunansu, amma karkace musu 'yan Salafiyyah don kuwa ba manhajin salafiyyar sukebi ba, sannan kada kace musu 'yan madakhila domin babu alaka ko kadan tsakaninsu da Sheikh Rabi'u binu Hadi Almadkhli
*WA IZA QULTUM FA'ADILU*
✍🏼
```Jameel A Kabo```
_*(ABU ZULAIKHA)*_
03-11-1441
26-06-2020