HIKAYA 2


*HIKAYA 2!!!*
.
.
*ALHERINE😀😀😀*
.
.
*DAGA ZAUREN*
.
*KITABU WAS SUNNAH*
.
.
*مجلس تعليم الكتاب والسنة*
📓📔
Watsaps
08036222795
09031200070
.
.
_Wannan itace Hikayarda mukace zamu gabatar karkashin Hadisinda manzon Allah (s.a.w) yace Shi mumini lamarinshi gaba daya alherine,_
.
.
_Azamaninda yashude anyi wani sarki wanda yake yawan tafiye tafiye, kuma al,adar sarkin shine duk sanda zeyi tafiya baya tafiya dakowa dagashi sewani bawanshi guda daya yake tafiya,_
.
_Watarana se sarkinnan tsautsayi yasameshi wanda har yarasa yatsan hannunshi guda daya,_
.
_Mutanen gari da fadawa kowa yanata zuwa yagaida sarki kuma ayimasa jajen rasa yatsar dayayi,_
.
_Zuwacan sega shima wannan bawan yashigo yagaida sarki sannan yace ranka yadade karka damu insha,allahu alherine,_
.
_Aikuwa ran sarki seyabaci😡😡, yace tayaya bala,i zesameni amma kuma kace alherine, sekawai sarki yasa aka kama wannan bawan aka kaishi bursuna aka rufeshi,_
.
_Amma bawannan lokacinda fadawa suka kamashi zasukaishi bursunan sekawai yakalli sarki yace babu komai insha,allahu Alherine,😀_
.
_Bayan kwana biyu sekawai wata tafiya takama sarki gashi kuma abokin tafiyannashi wato wannan bawan yana gidan yari,_
.
_Fadawa sukace afito dashine?? Se sarki yace Aa yau shikadai zeyi tafiyarsa baya bukatar dan rakiya,_
.
_Aka hadama sarki doki dakomai natafiya, yakama hanya, yanufi inda zashi,_
.
_Sarki yana cikin tafiya yashigo wani daji sekawai yaci karoda arnan daji suka kamashi suka daure,_
.
_Wayannan arnan suka tafi da sarki wani daki suka rufeshi,_
..
_Bayan kwana biyu se aka fitoda sarki akayimasa zindir aka kaishi wani daki, sukace yau jininka shine zamuba gunkinmu abun bautarmu dan haka yau zakayi bankwana da duniya😳😳😳😳,_
.
_Sarki yayi tsuru tsuru gashi adaure tsirara kuma yatabbatar cewa babu makawa yankashi za,ayi😭😭_
.
_Zuwacan sega wani katon mutum yazo daukeda sharbebiyar takobi tana kyalli, yazo yafuskanci sarki atsaye,😳😳😭😭_
.
_Zuwacan bayan yagama karema sarki kallo sekawai yayi tsaki ya tikama sarki dundu abaya, yace aikin banza, ashe dama kai nakasashshene, bakada yatsa daya😏😏,_
.
_Mutumin yace aikin banza wanene zeyankama abun bautarshi wannan musakin, yayi tsaki yace akwanceshi yawuce yabamu waje bamason musaki,_
.
_Aka kwance sarki suka koreshi,_
.
_Aikawai daganan sarki bema karasa inda zashiba sekawai yajuya yakoma gida,_
.
_Lokacinda sarki ya iso gida jama,a suka tarbeshi anata murna, se sarki yace aje afitoda wannan bawan daga jarun akawoshi,_
.
_Aikuwa ana zuwada bawa seyakalli sarki yace Alhamdulillahi har kadawo, seyace hakanma alherine,_
.
_Se sarki yace kai dakata, narasa dan yatsana kace alherine toh lallai nayarda alherine dankuwa kaji kaji abunda yafaru dani, lallai nayarda alherine rasa danyatsar danayi dankuwa inda ban rasa yatsarba aidatuni narasa raina😀😀_
.
_Bawa yagodema Allah yakara cewa lallai alherine,_
.
_Se sarki yace toh kaikuma lokacinda nace akaika gidan yari akulleka naji kace alherine, toh tayaya akayi shiganka gidan yari yazama alheri??_
.
_Bawa yace lallaikuwa babu shakka alherine, saboda duk sanda zakayi tafiya danikadai kake tafiya, amma wannan karon seka turani gidan yari wanda hakan shiyasa baka tafi daniba, kuma inda katafi dani lokacinda arnan dajinnan suka ga bakada yatsa ai kaga babu makawa ni zasu yanka tunda nidai lafiya kalau nake,😀😀,_
.
_Amma kaga cikin ikon Allah se nashiga gidan yari hakan yasa yazama alheri tunda gashi natsira da rayuwata,_
.
_Dajin haka se sarki yakwashe da dariya yace toh tunda hakanema daga yau na yantaka kazama da, kuma abokin shawarana,_
.
_Take anan bawa da sarki suka rungume juna suna fadin alherine😀😀_
.
.
_Wannan shiyasa malamai sukace inkaji manzon Allah yafadi wata magana koda baka fahimcetaba toh karkayi musu ko inkari amma tanada fa,ida,_
.
_Shiyasa manzon Allah yace akwai abun mamaki ga sha,anin mumini, komai nashi alherine,_
.
.
_Danhaka muma muke muku fatan alheri kuma komai kagani alherine matukar zakayi hakuri,_
.
.
*ALHERINE YAN,UWANA😀😀😀*
.
.
Domin samun shafinmu a Facebook sekushiga nan kuyi like
https://m.facebook.com/Kitabu-Wassunah-1522000298067561/-
Domin samun shafinmu na Telegram
https://t.me/joinchat/IqYRYUcyJstfI3sSYKPKsQ
Post a Comment (0)