SHIN ZAKI RAMA AZUMIN DA AKE BINKI KO KUWA ZAKI HAKURA KI SHIGA WUTA??



SHIN ZAKI RAMA AZUMIN DA AKE BINKI KO KUWA ZAKI HAKURA KI SHIGA WUTA??
.
.
*DAGA ZAUREN*
.
*MAJALIS - SUNNAH*
.
.
مجلس السنة
📓📔
09032091131
08067812397
.
.
Yau 24/ 10/ 1440 wanda yayi dai-dai da 16/ 06/ 2019.
=
=
_Godiya ta tabbata ga Allah, muna gode masa, muna neman taimakonsa, kuma muna neman tsarinsa daga sharrin kawunanmu da munanan ayyuakanmu. Hakika Wanda Allah ya shiryar Babu Mai 6atar dashi, Wanda ya 6atar Kuma Babu mai shiryar dashi. Kuma Ina Shaidawa babu abinda bautawa da Gaskiya sai Allah shi kadai, kuma ba shi da abokin tarayya. Kuma Ina Shaidawa Muhammad bawansa ne Kuma manzonsa ne._

_Bayan haka, wannan dan takaitaccen bayani ne ko ince tunatarwa ne zuwa ga yan uwana mata kuma iyayena, sakamakon yadda wasu suke barin ramuwar azumi har ta kai shekara da shekaru basu rama ba, wanda daga baya sai dai su dawo suna neman fatawar ciyarwa, lallai ya kamata kuji tsoron Allah, kuma ku dinga kwadayin falalar dake cikin azumin Ramadan, domin tabbas yawancinku bakusan falalar dake cikin azumi watan Ramadan ba, shiyasa wasunku suke neman fatawar ciyarwa, alhalin sunada ikon da zasu iya rama wannan azumin. Lallai kuji tsoron Allah ku sani cewa akwai ranar da zaki so ace kullum ki dinga yin azumin amma kuma wannan lokacin babu damar yi, saboda haka yanzu tun munada ranmu da lafiyarmu yakamata kuyi gaggawa ku azumci ramuwar da ake binku._

_Idan na rantse bazanyi kaffara ba cewa akwai wadanda ake binsu azumin shekaru biyar da suka wuce, wasu kuma sama da haka, domin na taba samun irin wadannan tambayoyin cewa ya za ayi a rama azumin shekaru biyar da ake binta, kuma wallahi yawancinsu da gan-gan suke bari ramuwa, ke yanzu har zaki iya yarda ki mutu Allah yana binki bashi? Yanzu ya kike ji idan kika hadu da mai shagon da ya baki bashin kayan miya? Ya kike ji idan kika hadu da mai kayan kwaliyyar da ta baki bashin kayan shafe-shafe? Ya kikeji idan kika hadu da mai turaren da ya baki bashi?_

_Ni dai na rantse da Allah kunya zakiji, da kuma faduwar gaba, wata ma guduwa zatayi bazata so ta hadu dashi ba. Ko ba haka bane?? Tho wannan fah dan Adam ne. Inaga kuma Allah ne yake binki? Wai shin kinada tabbacin cewa Zaki samu wanda zai rama miki bayan kin mutu? Kinada tabbacin cewa Allah zai yafemiki ne? Wallahi kiji tsoron Allah, kiji tsoron azabar Allah, kiyi kwadayin rahmar Allah kiyi gaggawa ki azumci azumin da ake binku. Ku sani Allah baya mantuwa, kuma wallahi sai kun biya._

_Inda zakusan wasu matan da gangan suke qin yi azumin shine, a wannan watan na shawwal wasu suna neman fatawar cewa *shin zan iya azumin sitta shawwal, alhali ana bina azumin Ramadan?*, Kunga anan indai ba da gangan take ba, meyesa bazata fara rama na farillah ba, kafin tayi na nafila?? Kunga wannan batasan falalar dake cikin watan Ramadan ba, kuma batasan illar da take ciki idan ta mutu bata rama ba. Saboda haka kuji tsoron Allah, kuyi gaggawa kuyi azumin da ake binku. Kada ki bari ki mutu baki rama ba, kuma wannan abinda kuke yana nufin cewa kamar kunsan bazaku mutu at anytime ba, domin da ace kinsan cewa zaki iya mutu at anytime, tho da bazaki bar azumin da ake binki baki rama ba._

_Sannan abu na karshe mu dage da yawan azumin nafila domin yanada falala sossai, domin akwai kofa acikin kofofin aljanna na masu yawan azumi kadai ne zasu shigeta, saboda haka mu dinga kwadayin wannan kofar, kuma mu dinga kwadayin rahmar Allah._

_Haka kaima kaji tsoron Allah ka dinga kokari kana azumin nafila koda na ranar litinin da alhamis ne kawai, domin wasu da dama daga cikin maza basuyi azumin sittu shawwal ba, ni naji da kunne na wani yana fadin cewa, tunda Allah yasa na gama azumin Ramadan da kyar, tho sai kuma idan wata Ramadan din tazo. Kunga wannan jahilci ne da rashin sanin falalar dake cikin azumin nafila._

_Allah Ubangiji ya taimake mu, ya kuma ba wadanda ake binsu azumin Ramadan, su samu su biya da wuri._
=
=
_Dan uwanku a musulunci_
°
*_✍Abdulrasheed Ibn Musa Abms_*
*_(ABU-MANAL)_*
°
°
.
Allah ta'ala yasa mudace
.
.
https://www.facebook.com/Zauren-Majalis-Sunnah-420869088334488/?referrer=whatsapp
.
ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.
Post a Comment (0)