Bayan na kawar maka da hankali, nasa ka fita daga hayyacinka, ƙarshe zaka rinka yin abubuwan da kai da mahaukaci baku da maraba (Bambanci)
Gani da daɗin sha'ani idan ka fara tu'amali dani. Dan zan sakaka a duniyar da kai kanka baka taɓa mafarkin akwai ta ba.
Zan sa mutane su bar ganin mutuncinka, ba tare daka ankara ba. Duk a cikin aikina ne zan saka iyaye da yawa fargaba, mutane da yawa suna ji suna gani sai dai su zuba mani ido ba yadda zasu yi dani.
Gani na kutsa na shiga ko ina, ban bar yara ba, ban bar manya masu ƙarancin tunanin rayuwa da makomarsu ta gaba ba.
In sa al'umma su ji tsoron baka shugabanci, saboda suna tunanin cewa ba zaka iya aikata komai ba.
In sa mutanan Unguwa su raba 'ya'yansu da kai, saboda suna ganin cewa zaka lalata masu yara, dan nasa suna maka wani kallo na daban, wanda basu ma yarda da kai ba.
A gidanku kuwa in sa ka dawo ƙarami, koda ka kai bishiyar kuka tsawo, shawarar kirki zan hana ayi da kai, saboda ana maka kallon babba a fuska, amma a aikace babban da bai san me yake yi ba.
Shin Wai wacece ni?
Ni ce ƘWAYA! 💊💊💊
Zaidu Barmo
17-June-2021
