BARA NA FADA MIKI GASKIYA

BARA NA FADA MIKI GASKIYA!

Idan na tabbatar da cewar kina sona ne saboda tarin dukiyar da Allah ya bani, to nima zan So ki na dan tsawon wani lokaci, shima kuma dole sai idan kin kasance kyakykyawa irin wadda duk inda na shiga dake za'a biki da kallo, tare da tayani murnar samun kyakykyawar mace kamar ki,

Bukatar ki a gareni daman shine dukiyar da nake da ita, to zan sakar miki ita har bayan munyi aure, zakici me kyau sannan kisha me kyau, bugu da kari ki zauna a matsugunni me kyawun da ya dara na inda kika fito.

Amman ko kadan kada kiyi gangancin tunanin samun girmamawa daga gareni, domin baki biyo hanyar samunta ba, kada kiyi zaton samun irin soyayyar da kullum kike gani a finafinan Hausa/India daga gareni, domin ban tanadar miki kalarta ba, kada ki tsammaci samun kulawa da tarairaya gami da mutunta iyaye da yan uwanki daga gareni, domin baki kasance daya daga cikin matan da suka cancanci wannan daga gareni ba!

Dukiya ta kike so, kuma gaki a cikinta kina wadaka da ita, jin wake wake da kallon finafinai a tashar Arewa24 sai su kasance masu tayaki zaman gidan, amman ki kwana da sanin bazan kasance me yi miki uzuri gami da kauda kai a duk lokacin da na sameki da aikatamin ba daidai ba, tabbas zaki tsinci abinda bakiyi tsammanin sa daga gareni ba!

Amman idan kika Soni saboda Allah, kika Soni a yanda nake bawai don na mallaki wani abu ba, kika So halittata da Dabiata amman ba shahara ko mulki ko tarin dukiyar da nake da itaba, tabbas zaki kasance mace mafi girman daraja a idona, zaki kasance mace ma'abociyar mallakar zuciyar mijinta, zaki kasance mafificiya a cikin fitattun matan dake rayuwa a karkara da birane a gareni!

Ba ke kadai ba, dukkan wanda yake da alaqa ta kusa ko ta nesa dake, tabbas zai tabbatar da nagartacciyar soyayya ta a gareki, duk yanda uzurirrika suka kai ga yin yawa a gareni, dole na samarwa da kaina lokacin ki na musamman, wanda zamuyi wasa tare, muci abinci tare, muyi wanka tare, 🙈 musha Ice cream tare, muyi wasan buya, uwa uba mu bautawa ubangijin mu a tare! Wannan alkawarina ne a gareki!

Inason naga an soni a a hakikanin yanda nake, bawai don wani abu wanda a kowanne lokaci zan iya rasashi ba!

Ga dukkan macen da ta karanta wannan sako, kada ki dauka labarine kawai wanda ya fito daga kasan zuciya ta, tabbataccen bayani ne nake baki wanda hakan shine a kudurce a kasan zuciyar kowanne namiji!

Na rantse da Allah zakisha mamaki a karshe, a wurin dukkan namijin da ya tabbatar da cewar kina sonshi ne don wani abu da yake dashi, ba don a hakikanin dan adamtakar shi ba!

Shawara ya rage naki! 🚶‍♂️

Post a Comment (0)