RAKA'OI BIYUN ALFIJR



RAKA'OI BIYUN ALFIJR
(Raka'atayy Alfajr)

Manzon Allah SAW yace: "Raka'oi biyu na Alfijr sun fi duniya da abin da yake cikinta alkhairi". [Muslim 725]

●Sunna ce
●Raka'oi ce guda biyu sauk'ak'a
●Ana yinta bayan bullowar Alfijr na gaskiya kafin a sallaci Sallar Asuba
●Ana yinta a halin tafiya ko zaman gida
●Ana karanta: Fatiha da Qulya ayyuhal kafirun a raka'ar farko, Ta biyun: Fatiha da Qul huwallahu Ahad. Ko Fatiha kadai a duka raka'oin
●Wanda ya shiga masallaci yayi ta, to ta wadatar masa yin Tahiyyatul masjid, in kuma yayi niyyansu a tare to hakan yayi kyau(اللجنة الدائمة/271-7)
●Wanda sallar asuba ta kubuce masa: zai fara sallatar Raka'atay fajr sannan yayi sallar asuba(Ibnul Bazz/Majmu'ul fataawa:377/11)
●Wanda ta kubuce masa yana da zabin ya sallaceta bayan sallar asuba ko jinkirta ta zuwa dagowar rana(Ibnul Bazz/Majmu'ul fataawa:373-11)

#Zaurandalibanilimi

TELEGRAM
https://t.me/Zaurandalibanilimi

INSTAGRAM
https://instagram.com/zaurandalibanilimii?igshid=emf6f90ssc24
Post a Comment (0)