TSARIN SALLAR MACE MAI HAILA BAYAN TA SAMU TSARKI



TSARIN SALLAR MACE MAI HAILA BAYAN TA SAMU TSARKI :-🌹

💖🥀Wannan shi ne tsarin da mace za tayi sallah bayan ta samu tsarki.

💖🥀(1) Idan mace ta samu tsarki kafin bullowar Alfijir. Zata sallaci magariba da isha'i sannan tayi Sallar asuba. 

💖🥀(2) Idan ta samu tsarki bayan bullowar Alfijir kafin fitowar rana. Zata sallaci asuba ne kawai.

💖🥀(3) Idan ta samu tsarki bayan bullowar rana to ba zata sallaci asuba ba sai dai ta fuskanci azahar.

💖🥀 (4) Idan ta samu tsarki bayan Sallar azahar kafin sallar la asar zata sallaci azahar ne kawai. 

💖🥀(5:)Idan ta samu tsarki bayan la asar to zata sallaci azahar da la asar. 

💖🥀(6) Idan ta samu tsarki bayan magariba kafin isha'i zata sallaci magarba kawai.

💖🥀 (7) Idan ta samu tsarki bayan isha'i zata sallaci magarba da isha'i.

👉A sanar da mata wannan a kuma yada sakon saboda muhimmancinsa. Allah ne mafi sani
Post a Comment (0)