RUBUTACCIYAR WAƘAR SHAKSIYYA

Yau kuma cikin ikon Allah ga shi mun kawo muku rubutacciyar waƙar shaksiyya daga bakin fasihin mawaƙi Aminu Ala 

SHAKSIYYA


Shaksiyya, shaksiyya shaksiyya ta
Shaksiyya ta faɗi ban gane ba
Wayyo ni, Wayyo ni, Shaksiyya ta
Yaya zan in kwashe ban ɓata ba.

Wawilun Wawilun babbar riga
Ga fili ga doki ga kau daga
Ga fili ga dokin ga me yanga
Ga fili an shaya ga mai burga
Ɗan halak ka fasa ba tsoro ba
Linzami ya zarce bakin kaza
Sabawa bai hana yankan kaza
An tirza an kasa yankan ƙarza
An guntsa an furzar saura harza
An tsaga an yanka be huda ba. 

Sunana ya ɓaci ban gane ba 
Martaba ta faɗi ban gane ba 
Kwarjini ya rushe ban gane ba 
Daraja ta babu ban aune ba 
Shaksiyya ta faɗi ban gane ba 
Nai faɗuwar tasa ban gane ba 
Hadarin kaka ni ne ban gane ba 
Ga dama ga hauni ban gane ba 
Ga ilimin addini be nuna ba 
Ga ilimin zamani be nuna ba 

Birgimar hankaka ce waƙata
Burgamin ƙasaita be ɗaukar ta
Sulke ne da fusaha ke saƙa ta
Lura ce da basira ke waye ta
Ban ware ɗan sarki ko bawa ba
Yaushe ne, Yaushe ne zan san kaina?
Yaushe ne zan gane ciwon kaina?
Yaushe ne zan dinga kishin kaina?
Yaushe ne zan kare addinina?
Yaushe ne ranar nan ban gane ba. 
Post a Comment (0)