SIRRIN ZUCIYA


SIRRIN ZUCIYA


Masoyi nawan sirrina,
Ƙaunar ka nake mai sona,
Murmushinka abun so ruhina,
Zuciya tawa duk na ba ka,

Har ma da ruhi sahibina,
Na ma mallaka maka duk kaina,
Ka riƙe ni amana angona,
Ka ji nawa É—an albarka,

Iyayena sun san da matsayinka,
A zuciyata, kuma suna yabon ka,
Hali na gari ag gare ka,
Fatan alhari nake maka,

Habibi yaushe za ka aiko?
Sadakina a yi mana baiko,
Kula da ni wajenka ba sai na yi roko,
Iyaye sun saka mana albarka,

Ga hannuna kawo naka,
Mu je lambu kauna mu tsinka-
Furen ƙauna da soyayarka,
Mu yo rangaji mu tattaka.


©Real Nana Aisha
2-06-2021
Post a Comment (0)