Ramadaniyyat 1442H [27]
Dr Muhd Sani Umar (Hafizahullah)
Sahabban Annabi (SAW) Su Ne Masu Fatan Rahmar Allah
___________________________
1. Allah (SWT) yana cewa: "Lalle wadanda suka yi imani da kuma wadanda suka yi hijira, kuma suka yi jihadi don Allah, wadannan su ne suke fatan rahamar Allah; Allah kuwa Mai yawan gafara ne, Mai yawan jin kai". [Al-Bakara, 218].
2. A nan Allah (SWT) ya bayyana cewa, wadanda suka mika wuya ga gaskiya, suka yi imani, suka kuma yi hijira daga garuruwansu don tsira da addininsu, sannan suka yaki makiya Allah don taimakon addininsu da daukaka kalmar Allah ((); to wadannan su ne suke sa ran samun rahamar Allah da Karramawarsa, kuma lalle Allah zai girmama su ya ba su ladan da suke fatan su samu a wurinsa, saboda shi Allah mai yafe zunubbai ne, mai rahama ne ga bayinsa, yana musu gwaggwabar sakayya a kan ayyukansu, a duniya da lahira.
3. Wadannan bayi na Allah su ne zababbu a cikin wannan al'umma, sannan kuma Allah ya tabbatar da cewa, su ne masu kyakkyawan fata daga Allah, don su sami dacewa da abin da suke kauna, su kuma kubuta daga abin da suke ki.
4.Wanda duk ya san dalilin saukar wannan ayar da wadda ta gabace ta, ba zai yi tababa ba a kan cewa, wannan ayar ana nufin sahabban Annabi (SAW) da suka yi hijira tare da shi zuwa Madina.
5. Dalilin saukar wannan aya kuwa shi ne, wata rana Annabi (SAW) ya aika da wata karamar runduna karkashin jagorancin Abdullahi dan Jahshi, sai suka gamu da wani mushriki ana ce masa Ibnul Hadhrami, sai suka kashe shi, ba su san cewa a watan Rajab suke ba. Sai mushrikai suka rika fada wa Musulmai cewa: “Kun yi kisa a cikin wata mai alfarma”. Sai Allah ya saukar da fadarsa: “Suna tambayar ka game da wata mai alfarma, yin yaki a cikinsa.” Daga nan sai kuma wasu suka rika cewa: “Ko ba su da laifi, to amma kuma ba su da lada.” Sai Allah ya saukar da fadarsa: “Lalle wadanda suka yi imani da kuma wadanda suka yi hijira kuma suka yi jihadi don yada kalmar Allah, wadannan su ne suke fatar samun rahamar Allah; Allah kuwa mai yawan gafara ne mai yawan jin kai.” [An-Nasa’i, As-Sunan Al-Kubra #8803, Abu Ya’ala #1534, At-Tabarani #1670].
6. Ba shakka Musulmi sun yi farin ciki da saukar wannan ayar, domin ta fitar da su daga duk wata damuwa da suke ciki, da tsoron da ya cika musu zuciya game da abin da ya faru ga rundunar Abdullah dan Jahshi.
7. Don haka kanmu tsaye za mu tabbatar da cewa, a nan Allah ya yi kyakkyawar shaida ga sahabban Annabi (SAW) ya kuma tsarkake musu zukatansu ya tabbatar da kyakkyawar niyyarsu, kuma ya ba da shaida a kansu cewa, duk abin da suke aikatawa, suna aikata shi ne don fatan samun rahmar Allah. Wannan kuwa babban dalili ne mai tabbatar da cewa, su mutane ne masu cikakken ikhlasi.
https://t.me/miftahul_ilmi
