SHIN MIJI NA ZAI IYA AUREN MATAR MAHAIFI NA, WACCE BA ITA TA HAIFE NI BA?



SHIN MIJI NA ZAI IYA AUREN MATAR MAHAIFI NA, WACCE BA ITA TA HAIFE NI BA?

https://chat.whatsapp.com/KeXayNmsBie671pMAKT9xN

*TAMBAYA*❓

Aslm Allah yaqarawa Mlm lpy Da Nisan kwana Mae albarka ameen
Dan Allah Mlm shin ya halatta mijina ya auri matar mahaifina bayan sun rabu da mahaifina muyi zaman kishi nida ita


 *AMSA*👇

Wa alaikumus salamu wa rahmatullahi wa barakatuh. Alhamdu lillahi rabbil alamin wassalatu wassalamu ala rasulillahi wa ala alihi wa sahbihi ajma'in. 

Ya halasta mijin ki ya auri matar mahaifin ki, kuma har kuyi zaman kishi da juna a gida daya tare, ko gidaje daban, in dai ba ita ce ta haife ki ba ko ta shayar da ke ba. Hakan babu laifi, domin ita matar suruki wacce ba ita ta haifi matar mutum ba, ajanabiyyar sa ce. Sannan bata cikin lissafin matan da Allah ya haramta ma maza su aura. Wacce Allah yace ya haramta, ita ce uwa ta tsatso ko ta shayarwa 

(وَأُمَّهَاتُ نِسَائِكُمْ) [النساء:23] 

(وَرَبَائِبُكُمُ اللَّاتِي فِي حُجُورِكُمْ) [النساء:23] .

(وَحَلائِلُ أَبْنَائِكُمُ) [النساء:23] .

Ga misali nan, an samu a tarihin Sahabbai Abdullahi Bn Ja'afar ya auri yar Ali Bn Abi Talib radiyallahu anhum wacce ba mahaifiyar matar sa ba.

Allah ya baku hakurin zama da juna na yau da kullum. Shi yasa bai halatta miji ya kebe da kishiyar surukar shi ba, ko kuma matar mahaifin matar sa wacce ba ita ta haife shi ba, haramun ne, domin ajanabiyyai ne ga juna, ma'ana akwai aure tsakanin su.

Wallahu ta'ala a'lam.

 *_Amsawa_* :

 *Malam Aliyu Abubakar Masanawa*

Zaku iya samu wannan group na Facebook ta wannan hanyar👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Join us on Facebook🖕
Post a Comment (0)