HIKAYA 1



*Assalamu,alaikum*
:
*HIKAYA*
:
*DAGA ZAUREN*
;
*KITABU WAS SUNNAH*

*مجلس تعليم الكتاب والسنة 📔📓*
:
:
_Labarin wasu ma,auratane guda biyu mata da miji_
:
_Kuma abun Sha,awa da matar da mijin dukansu hafizaine mahaddatan Qur,ani_
:
_Wadannan mutane suna zamansu cikin jin Dadi da kwanciyar hankali_

_Kwatsam rannan Se malam yacewa malama inaso zan kara aure_
:
_Malama tace akanme???😳_
:
_Se yace Allah ne yace inkara😃_
:
:
_Tace infa kace Allah ne yace ka kara toh Kenan maganar tana cikin Alqur,ani_
:
_Malam yace eh tana ciki_
:
_Tace toh karanto ayar inji??_
:
_Kawaise malam ya kawo ayarda Allah yace idan kun tashi zakuyi aure toh Ku auri mata bibbiyu ko uku ko hudu_
 *ﻓَﺎﻧْﻜِﺤُﻮﺍ ﻣَﺎ ﻃَﺎﺏَ ﻟَﻜُﻢْ ﻣِﻦَ ﺍﻟﻨِّﺴَﺎﺀِ ﻣَﺜْﻨَﻰ ﻭَﺛُﻠَﺎﺙَ ﻭَﺭُﺑَﺎﻉَ😃_*
:
:
_Se malama tace toh ai kai banda kai yace dankuwa yace wadanda zasuyi adalcine kaikuma bazakayiba😃_
:
:
_Malam yace waye yace miki bazanyi adalciba?😡_
:
_Tace Allah ne yagayamin_
:
_Yace indai Allah ne yagaya miki toh kenan maganar tana cikin Alqur,ani_
:
:
_Tace kwarai kuwa tana ciki_
:
_Malam yace karanto inji👂👂👂_

:
:
_Aikuwa semalama tajanyo ayarda Allah yace Bazaku taba iya yin adalciba tsakanin maatayenku koda kuwa kunso yin hakan َ_
*ﻭَﻟَﻦْ ﺗَﺴْﺘَﻄِﻴﻌُﻮﺍ ﺃَﻥْ ﺗَﻌْﺪِﻟُﻮﺍ ﺑَﻴْﻦَ ﺍﻟﻨِّﺴَﺎﺀِ ﻭَﻟَﻮْ ﺣَﺮَﺻْﺘُﻢْ*
:
:
_Malam yayi dariya😃 yace aikece baki fahimci ayar dakyauba_
:
_Malama tace toh fahimtar dani👂👂👂_
:
_Yace ana nufin bazakaji yanda kakeso amarya kuma hakane daidai irin sonda kakema uwargidaba. Dole zakafi son wata aciki😃_
:
:
_Tace ahaka kafahimci ayar? 😏_
:
:
_Yace eh😃_
:
_Tace toh kaje kayi aure Allah yasa adace 😃_
:
_Yace ameeen😃_
:
_Aikuwa mallam seyaje yayo aure kuma yasake auro wata takwararsu wato hafiza itama tahaddace qur,ani tsaf👳_
:
_Yakawota gida._
:
_Bayan ango yagama shan amarci da amarya harna tsawon sati daya_
:
:
_Rannan seya kira uwar gida zuwa dakin amarya danufin zeyi musu nasiha dakuma bayanin yanda za,a raba girki_
:
_Aikuwa malam yana fara jawabi se karaf uwar gida tace Daya kenan☝_
:
_Malam ya banka mata harara amma becemata komaiba😏_
:
:
_Ranshi abace yacigaba da bayani har yagama_
:
:
_Yana gamawa seyace amarya ko kinada magana?😀_
:
_Karaf uwar gida tace biyu✌_
:
_Malam yafusata yace mekike nufi ina magana kina wani daya biyu??😡😡😡😡_
:
:
_Setace yi hakuri ina kirga yawan rashin adalcinda zakayimin ne kafin mutashi😫_
:
_Mallam yace yanzu har nayi miki rashin adalci azamannan??😳_
:
_Tace eh aidama tun farko seda nagaya maka bazakayi adalciba😫_
:
:
_Seyace toh gayamin rashin adalcin danayi miki?_
:
_Tace nafarko yaune kagama kwanakinka adakin amarya ko??_
;
_Yace eh_
:
_Tace nida amarya wacece babba??_
:
_Yace kece👉_
:
_Tace tunda nice babban wannan zaman damukeyi yanzu adakinwa yakamata ayishi??😩_
:
_Yace naki👉_
:
:
_Tace toh yanzu adakina Muke??_
:
_Yace Aa🙈_
:
_Tace toh kaji rashin adalci nafarko_
:
_Nabiyu lokacinda kagama maganarka tunda nice babba aini yakamata kafara bani dama inyi magana shin kayi haka???😏_
:
_Yace Aa🙈_
:
:
_Setace toh kaji nabiyu_
:
:
_Jin haka se malam yace toh tunda hakane bari inyi adalci mukoma qur,ani_
:
_Uwargida kinyarda mukoma kur,ani?_
:
;
_Tace Eh😃_
:
_Kefa amarya kin yarda?_
:
_Tace kwarai😃_
:
:
_Yace tsakaninke uwar gida dake amarya. Duk wacce takeda dalili acikin kur,ani itace zata fara magana toh tabamu dalilin setayi magana😃_
:
_Yana rufe baki sai amarya tayi wuf tadaga hannu☝_
:
_Uwar gida itama karaf seta DAGA hannu👆_
:
:
_Malam yace toh munajinki uwargida bamu dalili_
:
_Aikuwa caraf setace Allah yace wassabikuna...... ْ_
*ﻭَﺍﻟﺴَّﺎﺑِﻘُﻮﻥَ ﺍﻟﺴَّﺎﺑِﻘُﻮﻥَ*
_Ma,ama wayanda suka Riga sune suke kangaba kuma wayannan sune makusanta acikin aljannar ni,Ima😃_
:
:
_Mallam yace kefa amarya bamu naki dalilin_
:
_Aikuwa amarya tace Allah yace Walal akhiratu...... َ_
*ﻭَﻟَﻠْﺂﺧِﺮَﺓُ ﺧَﻴْﺮٌ ﻟَﻚَ ﻣِﻦَ ﺍﻟْﺄُﻭﻟَﻰ*
_Takarshe tafimaka alheri akan tafarko😃_
:
_Mallam take yajike dagumi yarasa abunda zegaya musu😳😳😳😳_
:
_Zuwa can shima mallam dayake arammane gangaran seya mike_
:
_Yace dake amarya👉_
:
_Da uwar gida👉_
:
_Dukanku kuji tsoron Allah dan kuwa yace Qul innal awwalina...._
*ﻗُﻞْ ﺇِﻥَّ ﺍﻟْﺄَﻭَّﻟِﻴﻦَ ﻭَﺍﻟْﺂﺧِﺮِﻳﻦَ ‏(49 ‏) ﻟَﻤَﺠْﻤُﻮﻋُﻮﻥَ ﺇِﻟَﻰ ﻣِﻴﻘَﺎﺕِ ﻳَﻮْﻡٍ ﻣَﻌْﻠُﻮﻡ*
_Kagaya musu lallai Dana farkon Dana karshen tabbas zamu taraku amikati ranar kiyama***_
:
:
Allah yasa mudace
:
_Allah yasa kur,ani yazama hujjarmu ranar alkiyama_
:
_Yan,uwa kunjidai amfanin ilimi ko Mutashi munemi ilimi yan,uwa_
:
_Yanzu wannan inda akwai jahili acikinsu karamin takaici zegani***_
:
:
*DAGA ZAUREN*
:
*KITABU WAS SUNNAH*
:
*مجلس تعليم الكتاب والسنة 📔📓.*
Watsaps
08036222795
09031200070
-
Domin kasancewa damu a shafin Telegram
https://t.me/joinchat/IqYRYUcyJstfI3sSYKPKsQ
Post a Comment (0)