TARIHINMU MADUBINMU(01)




TARIHINMU MADUBINMU(01)
a rana irin 4 ga watan ramadan

💡>1 Ah/623 CE:Annabi saw ya tura rundinar farko a musulunci sun kasance mutum 30 ne karkashin jagorancin Hamza bin Abdulmudallib RA don tare wani ayari na kuraishiya daya hada da mutum 300 karkashin jagorancin Abu Jahl.

💡>53 Ah/673 CE:rasuwar kwamandannan Ziyad bin Abihi wanda ya kasance gwamnan garin Basra a Iraq da Khurasan(Afghanistan) a zamanin Mu'awiya bin Abi Sufyan RA.

💡>238 Ah/858 CE:rasuwar malaminnan masanin fikihu Abu marwan Abdulmalik bin Habib Al-qurduby Al-maliky Al-andalosy.

💡>454 Ah/1062 CE:haihuwar malamin hadisinnan Abul Kasim Isma'il bin Ahmad bin Umar Assamarqandy.

💡>512 Ah/1118 CE:kubucewar garin Saraqusda (Zaragoza) a kasar Andalos(Spain da Portugal) daga hannun musulmai zuwa hannun kirstoci bayan musulmai sun shafi karni 4 suna mulkar garin.

💡>570 Ah/1175 CE: karbo garin Ba'alabak (Baalbek) a Lebanon da sarki Salahuddin yayi daga hannun mayakan kirstocin yamma(crusaders) a hanyara ta 'yanto Qudus daga hannunsu.

💡>666 Ah/1268 CE:'yanta garin Antakya a Turkey daga hannun mayakan kirstocin yamma (Crusaders) karashin jagorancin sarki Azzahir Bibars.

💡>795 Ah/1393 CE:rasuwar masanin hadisinnan Imam Ibnu Rajab Al-hanbaly babban mamalami a zaminsa.

💡>1073 Ah/1663 CE:daular Usmaniyya tayi shelar yakar Germany sakamakon karya wasu sharuda da sukayi a yarjejeniyar sitvatorok bayan shafe shekara 56 da yin wannan yarjejeniya.

💡<1363 Ah/1944 CE:rasuwar khalifan karshe a daular Usmaniyya(mai cikakken cikakken iko) Khalifa Abdulhamid II a garin da aka koresa bayan yan Free Mason da karnukan turawa sunyi masa juyin mulki da sa hannun turawa da yahudawa yan Zionism sakamakon kin yarda da yayi ya siyarmusu da Palestine da kuma kokarin farfado da daular Usmaniyya,anbinneshi a garin Madina.

#Abdurrahman muhd Sani Umar 

https://t.me/miftahul_ilmi
Post a Comment (0)