YANDA AKE CIYAR WA, AMADADIN AZUMI



YANDA AKE CIYAR WA, AMADADIN AZUMI
===================
Assalamu alaikum waramatullah, inaso Asanar Dani kamar Yaya ake ciyarwa din?
=
=
Wa'alaikumussalam
Ciyarwa abune mai sauqi, kamar yanda musulunchi gaba dayansa sauqi ne
=
Ga Wanda laruri yakamashi bazai iya azumiba, kuma azumin ya wajaba akansa, To sai ya chiyarda marar qarfi mutum daya Amadadin Azumi Daya.
     Na abinda yake chi madaidaichi na gidansa, batare da Tsanan tawaba, ba kuma qaranchi, Amma lalle amfison kachiyar daga irin abinda kuke ciki, kaman yanda Aka tambayi Annabi sallallahu alaihi wa sallam ya bada amsa, da "kada ku chiyar dasu ( marassa qarfi ) da abinda ku bakwa chi" kamar Yanda imam Ahmad ya futar da hadisin, haithami ya ingantashi, Ibn kathi ya kafa hujja dashi cikin Tafsrin sa, qarqashin [267 baqra ].

Son samu abashi a dafe, idan babu dafaffe, abashi da kayan dafi!

@Tsoho/Tsohuwan da basa iya azumi, suna iya chiyarwa ko su sa yayan su, su ciyar musu, idan basuda hali.

@marar lafiyan da aka ebe Tsammanin Warkewa, Alhalin yana hankalin sa

@mace mai ciki ko shayar wan da bazata iya ba, saboda Tsoron kanta da abinda ke.tare da ita ( Da ) seta chiyar wallahu a,alam

Ibn kathir 1/320...
Wallahu a,alam
============
06-09-1442
18-04-2021
@zauren
Al-khulafa'urrashiidun

#Telegram T.me/joinkhulafa

# Facebook.com/khulafaurrashiidun

Youtube
https://youtu.be/VMoOV983sz4
Post a Comment (0)