DAGA CIKIN LADUBBAN KWANCIYA BACCI (02)



DAGA CIKIN LADUBBAN KWANCIYA BACCI (02)

Da Sunan Allah Mai Rahma Mai Jinƙai

3. YIN ALWALA: Yana Daga Cikin Ladubban Kwanciya Bacci Mutum Yayi Alwala Kafin Zuwa ga Shimfiɗarsa. Hadisi Ya Tabbata Manzon Allah (ﷺ) Yace da Barra'u bn Azib:

(إذا أتيت مضجعك فتوضأ وضوءك للصلاة)
{متفق عليه}

 “Idan Zakaje Shimfiɗarka, To Kayi Alwala Irin Alwalar Da Kakeyi Idan Zakayi Sallah".
(Bukhari da Muslim)

Yana Daga Cikin Fa'idar Kwanciya Bacci Da Alwala, Shine Samun Addu'ar Mala'iku ga Wanda Ya tsarkake Jikinsa Yayin Kwanciya Baccin. Hadisi Ya Tabbata Manzon Allah (ﷺ) Yana Cewa:

عن عبد الله بن عمر رضى الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: (من بات طاهراً بات في شعاره ملك، فلا يستيقظ إلا قال الملك: اللهم اغفر لعبدك فلان، فإنّه بات طاهراً)
(رواه إبن حبان)

An Kar6o Abdullahi bn Umar (ra) Yace: Manzon Allah (ﷺ) Yace: “Duk Wanda Zai Kwanta Bacci Yana Cikin Tsarki, Zai Kwanta Da Wani Mala'ika a Gefensa, Bazai Farka ba Face Mala'ikan Yace: (YA ALLAH KA GAFARTAWA BAWANKA WANE, DOMIN YA KWANTA NE CIKIN TSARKI)".
(Ibn Hibban Ya Ruwaitoshi)

4. KWANCIYA TA BANGAREN DAMA: Bayan Kammala Alwala, Ladabi Na Gaba Da Musulmi Zaiyi Kafin Bacci Ya Ɗaukeshi Shine Kwanciya ta 6angaren Jikinsa Na Dama. Manzon Allah (ﷺ) Ya Umurci Sahabinsa Barra'u Da Kwanciya Ta Gefen Dama Yayin da Yazo Kwanciya Bacci, Inda Yake Cewa:

(إذا أتيت مضجعك فتوضَّأ وضوءك للصلاة، ثم اضطجع على شقِّك الأيمن.....)

“Idan Ka Iso Shimfiɗarka, Kayi Alwala Irin Alwalarka ta Sallah; Sannan Ka Kwanta ta 6angaren Jikinka Na Dama.......

Anan Zan Dakata Sai Mun Haɗu a Rubutu Na Gaba Insha Allah

ALLAH KA SANYA MU CIKIN BAYINKA MASU BIN SUNNAR ANNABINKA (ﷺ)

سُبْحَانَكَ اللَّهُمَّ وَبِحَمْدِكَ، أَشْهَدُ أَنْ لا إِلَهَ إِلا أَنْتَ، أَسْتَغْفِرُكَ وَأَتُوبُ إِلَيْكَ

✍🏼Abu Aysha Al-Maliky

TELEGRAM:
https://t.me/joinchat/OOh5_RUljMIixFLQgNCDyg
Post a Comment (0)