RIMTSE IDON KA, KADA KA YARDA KA SAƁA MA ALLAH ARANAR EID.



RIMTSE IDON KA, KADA KA YARDA KA SAƁA MA ALLAH ARANAR EID.

Imam Al-Wakee'u Allah ya masa rahama yake cewa "Watarana ranan eid mun fita tare da Imam Sufyanus Sauri sai yake cewa; "Farkon abunda zamu fara yi awannan wunin namu shine mu rimtse idanunmu (kada mu sake dagangan mu kalla haramun)".

الورع لابن أبي الدنيا 

Imam Alhassanul basri Allah ya masa rahama yana cewa "Duk wani wuni da ba'a sabawa Allah a cikinsa ba to ya zama ranar eid, hakanan duk wani wuni da mumini zai kebanceshi da da'ar Allah da Ambatonsa da yi masa godiya to wannan wunin ta zama eid".

لطائف المعارف 

TAMBIHI
Yaku yan'uwa mata kuji tsoron Allah, ku sani ranan eid ba ranar sharholiya bane, ba ranar sabawa Allah bane, ku sani mala'ikun da suke rubuta ayyukan bayi basa daukar hutu, kullum suna cikin aiki, yanzu ke baza kiji kunya ba a ranar eid arubuta sunan ki cikin wadanda suka sabawa Allah a irin wannan rana mai girman falala da daraja a musulunci??
 Ya ku yan uwa samari kuji tsoron Allah, baya daga cikin murnan sallah shirya party, Allah bai yarda ba Manzon Allah bai yarda ba, dan haka kuji tsoron Allah wannan haramun ne. 

Allah ya amsa mana ibadunmu ya gafarta mana kurakurenmu.

#Zaurenfisabilillah

TELEGRAM:
https://t.me/Fisabilillaaah

FACEBOOK:
https://www.facebook.com/Fisabilillaaah/
Post a Comment (0)