SALLAR ISTIKHARA
●Istikhara shine neman zabin Allah a kan wani al'amari na ka, ya zaba maka abin da yake shine ya fi alkhairi a gareka ta hanyar yin sallah da addu'ar da Sunnah ta koyar na Istikhara.
●Sunnah ne yin Istikhara, kuma a na yin ta ne ga abun da yake halal, kamar kasuwanci, sayan wani abu, neman aure, neman aiki da sauransu
●Idan mutum ya yi nufin yin wani abu, zai fara neman shawaran kwararru kuma amintattu masana a game da al'amarin.
●Mutum zai yi sallah raka'a biyu na nafila, sannan ya karanta Addu'ar.
Addu'ar Istikhara shine:
💧اللهم إِنِّي أَسْتَخِيرُكَ بِعِلْمِكَ، وَأسْتَقْدِرُكَ بِقُدْرَتِكَ، وَأَسْألُكَ مِنْ فَضْلِكَ الْعَظِيم، فَإِنَّكَ تَقْدِرُ وَلا أَقْدِر، وَتَعْلَمُ وَلا أَعْلَم، وَأَنْتَ عَلاّمُ الغُيوبِ، اللّهُمَّ إِنْ كُنْتَ تَعْلَمُ أَنَّ هَذَا اْلأَمْرَ- (وَيُسَمِّي حَاجَتَهُ) - خَيْرٌ لِي فِي دِينِي وَمَعَاشِي وَعَاقِبَةِ أَمْرِي- أو قال: عَاجِلِهِ وَأَجِلِهِ- فَاقْدُرْهُ لِي وَيَسِّرْهُ لِي ثُمَّ بَارِكْ لِي فِيهِ، وَإِنْ كُنْتَ تَعْلَمُ أَنَّ هَذَا اْلأَمْرَ شَرٌ لِي فِي دِينِي وَمَعَاشِي وَعَاقِبَةِ أَمْرِي، فَاصْرِفْهُ عني وَاصْرِفْنِي عَنْهُ وَاقْدُرْ لِي الْخَيْرَ حَيْثُ كَانَ ثُمَّ أَرْضِنِي بِهِ.
💧Allahumma inni astakhiiruka bi ilmika, wa astaqdiruka biqudratika, wa as'aluka min fadlikal azeem, fa innaka taqdiru wala aqdir, wa ta'lamu wala a'lamu, wa anta allamul ghuyuub, Allahumma inkunta ta'lamu anna hazal amra (sai ya ambaci bukatar na shi), Khairun liy fii deeniy wama'ãshiy wa ãqibati amriy faqdurhu liy wa yassirhu liy, thumma bãrik liy feehi, wa in kunta ta'lamu anna hazal amra sharrun liy fii deeniy wama'ãshiy wa ãqibati amriy fasrifhu anniy wasrifniy anhu, waqdur liyal khaira haithu kaana, thumma ardiniy bihi.
FASSARAN ADDU'AR: Ya Allah Ina neman zabinka domin iliminka, kuma ina neman Ka ba ni iko domin Ikonka, kuma ina rokonKa daga falalarKa Mai girma, domin Kai ne mai iko, ni ba ni da iko, kuma Kai ne Masani, ni kuwa ban sani ba, kuma Kai ne masanin abubuwan gaibu. Ya Allah! Idan Ka san cewa wannan al'amarin (Sai ya ambaci bukatan na shi) alkhairi ne a gare ni a cikin addinina, da rayuwana, da kuma karshen al'amarina, (A wata riwayar; da magaggaucin al'amarina da majinkircinsa) Ka kaddarta mini shi, kuma Ka saukake mini shi, sannan Ka albarkace ni a cikin sa. Idan kuma Ka san wannan al'amarin sharri ne a gare ni a cikin addinina, da rayuwana, da karshen al'amarina, (A wata riwayar; da magaggaucin al'amarina da majinkircinsa) Ka kawar da shi daga gare ni, kuma Ka kawar da ni daga gare shi, kuma Ka kaddarta mini alkhairi a duk in da ya ke, sa'annan Ka sanya mini yarda da shi".
____________________
●Shaykhul Islami Ibnu Taimiya(RA) ya ce: Mas'ala game da addu'ar Istikhara, shin a na yinta ne a cikin sallar ko bayan sallama a ke yinta? Ya ce: Ya halatta a yi addu'an a cikin sallar Istikhara ko a waninsa, kafin sallama ko bayan sallama, Amma addu'an kafin yin sallama shi ya fi falala, domin Manzon Allah(SAW) mafi yawa addu'oinsa kafin sallama ne, kuma mai sallah kafin sallama bai riga ya idar ba yana cikin sallah, to wannan shi ya fi kyau. Wallahu aalam
(الفتاوى الكبرى: ج2/ ص265)
●Wasu malamai kuma suna ganin yin addu'an bayan sallama shi ya fi, almuhim duk wanda ka yi yayi in sha Allah.
●A na yinta ne a lokutan da ba a hana yin nafila ba, Shaykh Ibnu Uthaimeen(RA) ya ce: "Sallar Istikhara idan na wani al'amarine na gaggawa da ba za a iya jinkirtashi zuwa lokacin hanin nafila ya fita ba to za a sallace ta haka nan, amma idan sababin yinta din zai yiwu a jinkirta (ma'ana al'amarin ba na gaggawa bane) to wajibi ne a jinkirta(har zuwa lokacin da ba a hana yin nafila ba).
(مجموع فتاوى ابن عثيمين 14/275).
●Wani ba ya yi ma wani Istikhara, kuma ba gani a ke yi a mafarki ba!
Duk wanda yayi shawara da amintattu kuma masana, sa'annan ya nemi zabin mahaliccinsa, kuma ya yi azama a cikin lamarinsa, to ba zai yi nadama ba, domin Allah madaukakin sarki Ya ce;
(وَشَاوِرْهُمْ فِي اْلأَمْرِ فَإِذَا عَزَمْتَ فَتَوَكَّلْ عَلَى اللهِ)
"Kuma ka shawarce su cikin lamarinka, idan kuma ka kuduri aniya, to ka dogara ga Allah".
#Zaurandalibanilimi
https://t.me/Zaurandalibanilimi
