FITOWAR CIYAWA A KABARIN MAMACI



TAMBAYA
========
👇
Assalamu alaikum malam ina wuni ya jama'a allah yakara daukaka ameen, malam tambayana shine mutun ne yamutu washe gari akaje kabarinsa aka samu ciyawa a kan kabarin wai hakan yana nunawa yasamu rahama kenan? Tambaya na 2 kuma yaya matsayin wanda yamutu da bashi  
Tsakaninsa da jama'a babu matsala duk wani yabo ya samu amman matsalan kawai bashine a kansa, nagode malam.

AMSA
=====
👇
1. Ba haka bane. Ciyawa tana Iya fitowa a ko ina. Musamman ma wurin da yake da lema ko Danshi. Sabida haka idan an zuba ruwa akan Kabarinsa Lokacin da Aka Binne shi. Akwai Yiwuwar Ciyawa ta fito.

2. Akwai Matsala mana.
 Mutumin da ya Mutu da Bashi Akansa. Gashi kuma ba'a sami wani daga cikin Danginsa ko Ahalinsa ya Biya masa ba. Shine ma kuwa yake cikin Matsala.
 Domin Manzon Allah saw ya tabbatar da cewar Wanda ya Mutu da Bashi Akansa ba zai shiga Aljannah ba. Har sai an Biya masa Bashin da Ake Binsa Gabaki daya. Har sai idan Wadanda yake bin bashin ne suka yafe Masa.
 Wanda a Farkon Musulunci Manzon Allah saw baya Yin Sallah ga wanda ake bi bashi. Har sai idan an samu wanda zai Biya Masa. Sannan ne zaiyi Masa sallah. Idan Kuma ba'a samu wanda zai Biya masa ba. Sai Yace ku Yiwa Dan Uwanku sallah.

Allah shine Masani.

✍️
ZAUREN FADAKARWA A SUNNAH MAZA MATA 08137783797

KUYI SUBSCRIBE TELEGRAM CHANNEL:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Post a Comment (0)