SHIN YA HALATTA NA BAWA IYAYE NA ZAKKAR FIDDA KAI?



*TAMBAYA*❓

Assalamu alaikum

SHIN YA HALATTA NA BAWA IYAYE NA ZAKKAR FIDDA KAI?


*AMSA*👇

وعليكم السلام ورحمة الله.
ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻟﻠﻪ ﺭﺏ ﺍﻟﻌﺎﻟﻤﻴﻦ ، ﻭﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻰ ﺳﻴﺪﻧﺎ ﻣﺤﻤﺪ ﻭﻋﻠﻰ ﺁﻟﻪ ﻭﺻﺤﺒﻪ ﺃﺟﻤﻌﻴﻦ، ﻭﺑﺎﻟﻠﻪ ﺍﻟﺘﻮﻓﻴﻖ،


Malamai sunyi ittifaaqi akan cewa bai halatta ba mutum ya bada zakkatul mafrud (Kamar zakkar fidda kai) ga wadanda nauyinsu ya rataya a wuyansa, kamar Iyaye da 'ya'ya.

An fada acikin _*Al-Mudawwanah (1/344):*_
Toh zakkar dukiya ta fa, su waye bai halatta Na bawa ba abisa ra'ayin IMAM MALIK??.

Yace; *Malik* yace: 
Karka bada ita ga duk wani ɗan'uwanka wanda nauyinsa yake akanka.

*Al-Shaafa’i* yace acikin _*Al-Umm (2/87):*_
Bazai bada (Zakkar dukiyarsa) ga Mahaifinsa ba ko Mahaifiyarsa ko Kakansa ko Kakarsa ba.

*Ibn Qudaamah (rahimahullah)* yace acikin _*Al-Mughni (2/509):*_
Babu daya daga cikin Zakkah ta farillah da za'a bawa Iyaye komai nisan nasabarsu (ma'ana Kakanni maza da Kakanni mata) ko 'Ya'ya komai Nisan nasabarsu (ma'ana Jikoki).

*Ibn Mundhir (rahimahullah)* yace:
Malamai sunyi ittifaaqi akan bai halatta ba abawa iyaye zakkah ba, a yanayi na kasancewar nauyinsu ya rataya a wuyansa. Saboda haka basu zakkah tamkar shine ya bawa kansa zakkah da kansa. Basu zakkah kamar Yana nufin su basa bukatar taimakon komai a wajensa ne, kuma babu nauyinsu na dawainiyarsu a wuyansa.

والله أعلم،

سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا انت أستغفرك وأتوب إليك.

Zaku iya samu wannan group na Facebook da na telegram ta wannan hanyar
TELEGRAM👇🏻
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Post a Comment (0)