TUNATARWA AKAN SALLAR JANAZA



TUNATARWA AKAN SALLAR JANAZA

        Yadda Ake Yin Sallar Jana'iza

1. KABBARA TA FARKO, Ana karanta Suraul-Fatiha ne kawai, banda wata sura, ko wata a'ya.

2. KABBARA TA BIYU, Ana karanta Salatin Annabi ne ba wani salati na daban ba.

3. KABBARA TA UKU, Ana yin addu'a ne ga mamacin, mace ne ko namiji.

4. KABBARA TA HUDU, Za kayi addu'a ne ga sauran al'ummar Musulmi Wadanda suke Raye da matattu.

DAN UWA KANA GAMAWA sai ka jira Liman ya yi sallama. 
Ita kuma sallamar guda daya ce tak! Kuma za ka yi ta ne a bangaren damanka.

Allah muke roko da ya kara tabbatar damu akan Sunnar Annabin Rahama, Manzon Allah (S.A.W). 

Akwai bukatar a yada Wan nan Sako Dan Allah ta Hanyar Share. domin 'yan uwa musulmai su karu. Allah yabada ikon Hakan Ameen.
Post a Comment (0)