ANNABI DA SAHABBANSA // 78



ANNABI DA SAHABBANSA // 78
.Mawallafi: Baban Manar Alqasim
.
YAQI YA ZO KAN ANNABI SAW
Mun sani tun a baya cewa an yi wa musulmai qawanya, kuma ba ma kowa tare da Annabi SAW sai mutum tara, kowa a lokacin ta kansa yake yi, ga kuma zancen kisar ma'aiki SAW, kenan maganar tuta ba ta ma taso ba kenan, duk da cewa mun fadi cewa qarfinsu ya fara farfadowa amma ya za a yi su taru wuri guda? Daidai wannan lokacin ne Annabi SAW ya daga muryarsa don isar da wannan wajibi, har da kasancewar ba shi ba ko waye ma zai yi wannan aikin sai ya baqunci lahira, bare kuma shi din ake nema, ya ce "Ku taru a nan, ni ne Manzon Allah!" Ai kuwa kafuran suka yo kansa da duk qarfin da suke da shi.
.
Amma wadannan mutunen 9 da muka ambata a baya su suka yi tsayuwar daka da duk qauna da qarfin da suke da shi wajen ba da kariya ga Annabi SAW, har dai aka kashe 7 a cikinsu, sai ya zamanto ba wanda ya rage tare da Annabi SAW sai Talha bn Ubaidillah da Sa'ad bn Abi-Waqqas (Bukhari 1/527, 2/581) hali mafi muni kenan da Annabi SAW ya sami kansa a ciki, su kuma mushrikai ba lokacin da suka ji dadi kamar wannan, don haka ba su yi wasa da wannan damar ba.
.
Sun mai da hankalinsu ne gaba daya wajen kawar da Annabi SAW, shi ya sa Utbah bn Abi-Waqqaas ya jefe shi da dutse a baki har ya yi wa fiqarsa ta qasa dake dama illa kuma ya raunata lebensa na qasan, Abdullah bn Shihaabiz Zuhriy shi ma ya sami damar yi masa rauni a goshi, Abdullah bn Qam'ah shi ma ya yi mummunar sararsa da takobi a kafada wadda ya yi sama da wata guda yana koka radadin wurin, don ma dai sulken da ke jikinsa ya dan taimaka sosai wajen hana kaifin takobin shiga jikinsa, ya sake kai masa wani bugun a saman kumatun har sarqa biyu na sulken ya shiga jikinsa.
.
Ya ce da Annabi SAW "Taba ka ji, ni ne Ibn Qam'a" shi kuma Annabi SAW ya fara share jini daga goshinsa yana cewa "Kai ma Allah ya kama ka" tabbas ya gama ya koma gida, a wani kiwo da ya fita saman dutse ya daure bunsurunsa a can, sai bunsurun ya dauke shi har ya fado qasa ya karairaye (Fat'hul Baari 7/373) nan dai Annabi SAW ya nemi gafarar Allah SW ga al'ummarsa sabo da aika-aikar da mushrikai suka yi ya ce "Ubangiji ka yi wa al'ummata gafara rashin sani ne" Muslim 2/108.
.
A qarshe dai wadannan gwaraza guda biyu wato Talha bn Ubaidillah da Sa'ad bn Abi-Waqqaas su kadai suka rage tare da Annabi SAW, abin tambaya ina sauran sahabban? Hankalinka ba zai taba dauka ba idan aka ce maka duk sun tsere, mutum biyu ne kadai suka yi saura a gaban mutum 3,000, tabbas sauran suna can a filin gwagwarmaya, tunanin cewa Annabi SAW yana cikin aminci, tunda kuma an ce an kashe shi ai ba wani nemansa da za a yi, duk da yake qarya ce sai dai ta sa muminai sun tsaya a kan duga-dugansu wajen yaqi.
.
Don ba sauran abin da kuma za su ji tsoron salwantarsa, Sa'ad da Talha duk Quraishawa sun san da su wurin iya harbi, da wadannan sahabban biyu din ne dai Allah SW ya tarwatsa mushrikai daga gaban Annabi SAW, mun fadi tazarar da take tsakanin Annabi SAW da sahabbansa, don haka kirar da ya yi ba wanda ya ji a cikin sauran sahabban bare ya yi yunqurin kawo agaji, duk da haka sun iso wurinsa bayan ya riga ya hadu da wannan jarabawar, a baya mun fadi yadda Abubakar, Umar da Aliy da wasu sahabbai suka fara shawagin neman inda yake bayan sun sami labarin cewa yana da rai.
.
A wannan yaqin ne musulmai suka yi yaqin da ba a taba yin irinsa ba a tarihi, don tun farkon fara yaqin ma ba yadda za a yi gwajin qarfi ta ko'ina tsakanin musulmai da mushrikai, amma kun ga yadda lamarin ya kaya, da a ce sahabbai da gaske ne sun gudu sun bar Annabi SAW da wata maganar muke yi ba wannan ba, amma haka Abu-Talha ya riqa miqa qirjinsa yana qoqarin kare kibau din da abokan gaba za su iya cillowa, a ranar sai da ya ci baka 3, ya yi qoqari suka yi ta kanguwa da garkuwa guda.
.
Ta baya kuma Abu-Dujana ya yi masa garkuwa haka kibau suka yi ta zuba a jikinsa ko gezau ba ya yi, sabo da sulke, shi kuma Haatib bn Abi-Balta'a RA ya bi Utba bn Abi-Waqqaas (Wanda ya karya wa Annabi SAW haqori) ya fille masa kai ya dauki dokinsa da takobinsa, dan uwansa Sa'ad bn Abi-Waqqaas shi ya yi ta burin haka amma Haatib ya riga shi, in ka bi sahabban nan da irin fafutukar da aka sha a Uhud, sai ka ga Badar suna ta yi, amma an sha ruguntsumin a Uhud.

Rubutawa:- Babban Manar Alqasim 
Gabatarwa:- Yusuf Ja'afar Kura

Daga 
*MIFTAHUL ILMI*

ZaKu iya Bibiyar Mu a 
Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml

Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi

WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248
Post a Comment (0)