HANYA MAFI SAUKI WAJAN TARBIYYANTAR DA 'YA'YA



HANYA MAFI SAUKI WAJAN TARBIYYANTAR DA 'YA'YA

🌴 Mahaifin da yake kashe television 📺 Lokacin da yaji kiran sallah kuma yake tafiya masallaci a lokacin, 'ya'yansa zasu taso su girma suna masu kiyaye sallah akan lokaci kamar mahaifinsu. 

🌴 Mahaifin da yake yin sallama yayin da zai shigo gida, kuma ya qwan'qwasa qofa ya nemi izinin shigowa, kuma yayi murmushi lkcn da zai shigo gida, 'ya'yansa ma zasu kasance masu yin sallama daneman izini dakuma yin fara'a a kullum. 

🌴 Mahaifin da yake girmama iyayansa kuma yake sumbatar hannayansu dan tausaya musu da jin qansu, wataran 'ya'yansa zasu sumbaci hannunsa kuma zasu dinga yimasa biyayya. 

🌴 Mahaifin da yake taimakawa matarsa cikin aikace'aikacan gida, yake tausayamata, 'ya'yansa zasuyi koyi dashi wajan taimakawa mahifiyar su da sauran mutane. 

🌴 Mahaifiyar da take sanya hijabi lkcn da zata fita, kuma take kiyaye sallah akan lokacin ta, kuma take karatun Al'qur'ani a cikin gidan ta, to zata sanya 'yarta ta kasance mai san saka hijabi, da kiyaye sallah akan lokaci dakuma karatun Al'qur'ani. 

🌴 Mata da mijin da suke fahimtar junansu, suke war'ware matsalolinsu a tsakaninsu, kuma ya kasance basa fada basa daga muryoyinsu musamman agaban 'ya'yansu, 'ya'yansu zasu so zama axikin wannan gidan, masu jin qan junansu, masu san junansu, kuma zasu kasance masu fahimtar junansu. 

🌴 Mahaifin da yake sadar da zumunci kuma yake kyautatawa 'yan uwansa da danginsa na kusa dana nesa, 'ya'yansa zasu koyi sada zumunci daga gareshi, da kuma kyautatawa da biyayya. 

🌴 Mahaifin da yake amfani da shawarar matarsa data 'ya'yansa awasu Al'amura na daban, kuma yake zama yayi hira tare dasu, 'ya'yansa da matarsa zasu shaqu dashi, kuma zasu dinga ganin girmansa, kuma zasu dinga yimasa biyayya. 

🌴 Mahaifin da yake yiwa 'ya'yansa gaskiya baya musu qarya acikin wasu Al'amura, 'ya'yansa zasu koyi yin gaskiya saga gareshi a cikin duk abinda zasuyi ko za'a sasu suyi. 

🌴 Mahaifin da yake cikawa 'ya'yansa Al'qawarinda yayi musu, 'ya'yansa zasu kasance masu cikawa mutane Al'qawarurrukan su. 

🌴 Iyayanda suke kula da tsafta dabi sannu'sannu da tsari a cikin Al'amura, 'ya'yansuma zasu kasance kamar su. 

FADAKARWA MAI MATUQAR MAHIMMANCI 👇

Yaku iyaye masu daraja kada ku nemi 'ya'yanku su aikata wani abu face kuma sai ya kasance kuna aikatashi tin kafin kusasu su aikata wannan abun, kuma kada ku hanasu wani abu face sai ya kasance kun fara hanuwa daga wannan abun, kada ka umarci danka dayin sallah Al'halin kuma kai bakayin sallar, kuma kada ki umarci 'yarki dajin kunya dasa hijabi amma kuma aikinki yana sabawa maganganun ki, hakika aikata hakan babban lefine a wajan Allah (swt) kuma aikata hakan yana sabbabawa mutum shiga wutar jahannama. 







✍️ ABU ABDURRAHMÃN
Post a Comment (0)