HUKUNCIN KARATA ALQUR'ANI BABU ALWALA :
TAMBAYA❓
Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuhu.
Malam tambaya nake dauke da ita game da karatun Alqur'ani. Shin wajibi ne sai nayi alwala kafin in karantashi? Ko kuwa zan iya yin karatun koda alwalata ta warware?.
Kuma shin menene hukuncin bama Qananan yara 'yan Islamiyyah cikakken Alqur'ani izu sittin (60) suna karatu dashi?
Allah shi Qara ma Malam lafiya da imani da ilimi da tsoron Allah.
AMSA👇
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.
Eh ya halatta ka zauna kayi tilawar Alqur'ani koda baka da Alwala. Amma sai dai yinsa da Alwalar yafi cikar kamalah.
Hujjah ita ce hadisin Nana A'ishah (ra) wanda take cewa "Manzon Allah (saww) ya kasace yana ambaton Allah aduk halin da yake ciki".
Da kuma hadisin da Imamul Bukhariy da Muslim suka karbo ta hanyar Sayyiduna Abdullahi 'dan Abbas (rta) wanda yace "Manzon Allah (saww) ya farka acikin dare sai ya kalli sararin sama ya karanta ayoyi goma na karshen Suratu Aali Imraan, Sannan ya tashi zuwa ga jakar ruwa wacce ke lanqaye, Yayi alwala daga gareta".
To kaga awancan hadithin na farko kenan yakan yi Zikiri da karatun Alqur'ani a kowanne yanayi.
Acikin hadisi na biyu kuma ana nufin cewa ya karanta ayoyi goman nan ne kafin yayi alwala.
Amma idan kana nufin halaccin daukar cikakken Alqur'ani kayi karatu acikinsa ne, to wannan bai halatta ba. Sai dai idan kana da alwala.
Hukuncin 'daukar cikakken Alqur'ani ga yaran da basu balga ba, duk daya kamar babba. Wato wajibi ne sai da alwala. Idan kuma aka bashi ya dauka alhali bashi da alwala, to laifin yana kan wanda ya bashi din.
WALLAHU A'ALAM.
Ku kasance damu domin ilimintarwa da Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177