HUKUNCIN MAGANIN KARKATO DA HANKLIN MIJI ZUWA GA MATARSA:



HUKUNCIN MAGANIN KARKATO DA HANKLIN MIJI ZUWA GA MATARSA:

*TAMBAYA*❓

Mijina ya kasance ba ya damuwa da ni, ko a wajan muamalar aure ba ya gamsuwa da ni, ga shi mai taurin kai da rashin sakin hannu da sauransu.

Muna haka sai na samu magani da zan sha don karkato da shi zuwa gareni.
Kuma maganin na gari ne da ake sha, a wajan shan kuma za a ambaci sunan mijin. 

mene hukuncin wannan.

*AMSA*👇

Maganin da mace za ta sha don kyautata alaƙarta da mijinta ya kasu gida biyu:

1- maganin da za ta sha don Æ™ara mata niima da za ta sa mijinta ya ji daÉ—in muamalar aure da ita. 
wannan babu komai idan ya kasance an haÉ—a shi ne da sinadarai halatattu kuma ba zai cutar da lafiyarta ba.

2- Magungunan da ake yi masu alaka da sihirce sihirce waÉ—anda za su juyo da hankalin miji zuwa ga matarsa ba don wani sababi na zahiri da ke É—aukar hankalin maza ba, kawai sai don tasirin wannan magani gareshi.
Irin wannan yana cikin ababen da ake kira (Attiwalah) = Mallakau ko bita-zai-zai, kuma hadisi ya tabbata daga Manzon Allah s.a.w cewa shirka ne.

A zahiri maganin da mai tambayar ta ambata ya fi kama da kashi na biyu (mallakau - Attiwalah) don kuwa maganin da za a ce sai kin ambaci sunan miji wajan shansa, akwai alamar ba wata niima zai kara miki da za ta sanya mijinki ya so ki ba ne, kawai dai za a sihirce shi ne ya so ki ba so na É—abia ba.

Duba da haka anfani da irin wannan maganin ba ya halatta.
Abin da ya kamata mai irin wannan matsalar ta yi shine ta duba ta ga sababin da ya sa mijinta ba ya shaawarta.
Idan ya zama sababin wata gazawa ce daga gareta ta wajan rashin gyaran jiki ko rashin kyakykyawar muamala to sai ta yi ƙoƙari ta gyara kurakuranta.
 Idan kuma ya kasance matsalar daga mijin ne sai ta lura sosai:
Ko dai ya zama wasu abubuwa ne suke ɗauke masa hankali sai ta bi hanyoyin da suka dace a shariance da hikima wajan nusar da shi kula da haƙƙin iyalansa.
ko kuma ya zama sihiri aka yi masa: to sai ta bi hanyoyin da suka dace da shariah wajan warware sihirin, ba ta hanyar shan irin wannan magani da shi ma yake É—aukar hukuncin sihiri ba, dmin ba a warware sihiri da sihiri.

*DAGA CIKIN HANYOYIN DA MACE ZA TA BI DON KYAUTATA ALAKA DA MIJINTA:*

1- Gyara jikinta a ko da yaushe.
2- Kyautata kalamanta da sanin abin da za ta fada a gabansa.
3- Lura da abin da ya fi so na abinci ko abin sha tare da tanadar masa shi gwargwadon iko.
4- Nuna ƙauna ga iyaye da yan uwansa.
5- Tarairayarsa da nuna damuwa da shi fiye da komai.
6- Nisantar abin da ba ya so wanda bai saɓawa sharia ba.
da sauransu...

Wallahu Aalam

Ku kasance damu domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Post a Comment (0)