SUNNAH NE..
Shaykh Muhammad Bin Saalih Al- 'Uthaymeen رحمه الله yace;
A lokacin da mutum yake gida to yana daga sunnah, Misali ya hada shayin sa da kanshi (ba sai ya umurci matarsa da tayi masa ba), ya dafa abinci idan ya iya, ya wanke duk wani abinda ke buƙatar a wanke shi, duk wannan Sunna ne.
Idan kunyi haka to kun sami ladan bin Sunnah, tare da kwaikwayon Manzo [ﷺ] da kuma ƙasƙantar da kanku ga Allaah - Mabuwayi da ɗaukaka.
Wannan kuma yana kawo soyayya tsakanin ku da iyalanku. Lokacin da matanku suka ga cewa kuna taimaka musu a ayyukan su za su ƙaunace ku kuma ƙimar ku a gare su za ta ƙaru, saboda haka, wannan zai zama babban fa'ida.
[SharhurRiyadh As-Saaliheen, (3/529) ]
Zaurenfisabilillah
Telegram:
https://t.me/Fisabilillaaah
Instagram:
https://www.instagram.com/zaurenfisabilillah/